Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 30–62

The Early Church

Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.

1,007 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’

  2. “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ”

  3. Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!”

  4. Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da tā da ƙura sama,

  5. sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka.

  6. Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”

  7. Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”

  8. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Bulus ya ce, “I.”

  9. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.”

  10. Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa.

  11. Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.

  12. Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.”

  13. Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.

  14. Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”

  15. Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”

  16. Bulus ya amsa ya ce, “’Yan’uwa, ai, ban san cewa shi ne babban firist ba; gama yana a rubuce cewa, ‘Kada ka yi mugun magana game da mai mulkin mutanenka.’”

  17. Bulus, da ya gane cewa waɗansu daga cikinsu Sadukiyawa ne sauran kuma Farisiyawa ne, sai ya ɗaga murya a Majalisar ya ce, “’Yan’uwana, ni Bafarisiye ne, ɗan Farisiyawa. Ana mini shari’a saboda begen da nake da shi a kan tashin matattu.”

  18. Da ya faɗi haka, sai gardama ta tashi tsakanin Farisiyawa da Sadukiyawa, taron kuwa ya rabu biyu.

  19. (Sadukiyawa suna cewa babu tashin matattu, babu mala’iku ko ruhohi. Amma Farisiyawa kuwa sun tsaya a kan cewa duk akwai.)

  20. Aka yi babbar hayaniya. Waɗansu daga cikin malaman dokokin da suke Farisiyawa suka miƙe tsaye suka yi gardama mai ƙarfi suna cewa, “Ba mu sami wani laifi a wurin mutumin nan ba. A ce wani ruhu ko mala’ika ne ya yi masa magana fa?”

  21. Gardamar kuwa ta yi tsanani har shugaban ƙungiyar sojan ya ji tsoro za su yayyage Bulus. Ya umarci sojoji su tafi su ƙwace shi ƙarfi da yaji daga wurinsu su kawo shi cikin barikin soja.

  22. Kashegari da dare Ubangiji ya tsaya kusa da Bulus ya ce, “Ka yi ƙarfin hali! Don kamar yadda ka yi shaida game da ni a Urushalima, haka kuma lalle, za ka yi shaidata a Roma.”

  23. Kashegari, Yahudawa suka ƙulla makirci suka kuma yi rantsuwa cewa ba za su ci ko sha ba sai sun kashe Bulus.

  24. Fiye da mutane arba’in ne suka ƙulla wannan makirci.

  25. Suka je wajen manyan firistoci da dattawa suka ce, “Mun yi babbar rantsuwa cewa ba za mu ci kome ba sai mun kashe Bulus.