- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 24:5kusan 60 M.
“Mun tarar da wannan mutum fitinanne ne, yana tā-da-na-zaune-tsaye a tsakanin Yahudawa ko’ina a duniya. Shi shugaban ɗarikar Nazarawa
- Ayyukan Manzanni 24:6kusan 60 M.
har ma ya yi ƙoƙari ya ƙazantar da haikali; shi ya sa muka kama shi.
- Ayyukan Manzanni 24:7kusan 60 M.
But the chief captain Lysias came upon us, and with great violence took him away out of our hands,
- Ayyukan Manzanni 24:8kusan 60 M.
Ta wurin bincika shi da kanka za ka gane gaskiyar game da dukan waɗannan zargin da muke kawo a kansa.”
- Ayyukan Manzanni 24:9kusan 60 M.
Yahudawa ma suka goyi bayan zargin, suna tabbatar cewa waɗannan abubuwa haka suke.
- Ayyukan Manzanni 24:10kusan 60 M.
Da gwamna ya yi masa alama yă yi magana, sai Bulus ya amsa ya ce, “Na san cewa ka yi shekaru da yawa kana mulki a wannan ƙasa; saboda haka ina farin ciki in kāre kaina.
- Ayyukan Manzanni 24:11kusan 60 M.
Da sauƙi za ka iya tabbatar cewa, bai fi kwana goma sha biyu da suka wuce ne na tafi Urushalima, domin yin sujada ba.
- Ayyukan Manzanni 24:12kusan 60 M.
Masu zargina ba su same ni ina gardama da kowa a haikali, ko kuma ina tā da hankalin jama’a a majami’u ko kuwa wani wuri dabam a cikin birni ba.
- Ayyukan Manzanni 24:13kusan 60 M.
Ba kuwa za su iya tabbatar maka ƙarar da suke yi yanzu a kaina ba.
- Ayyukan Manzanni 24:14kusan 60 M.
Amma na yarda cewa ina bauta wa Allah na kakanninmu a matsayin mai bin Hanyar da suke kira ɗarika. Na gaskata dukan abin da ya amince da Doka da yake kuma a rubuce cikin Annabawa,
- Ayyukan Manzanni 24:15kusan 60 M.
ina kuma da irin bege ɗaya ga Allah yadda mutanen nan suke da shi, cewa akwai tashin matattu masu adalci da masu mugunta duka.
- Ayyukan Manzanni 24:16kusan 60 M.
Saboda haka, ina ƙoƙari kullum in kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane.
- Ayyukan Manzanni 24:17kusan 60 M.
“Bayan ’yan shekaru da dama da ba na nan, sai na dawo Urushalima don in kawo wa mutanena kyautai saboda matalauta in kuma yi sadaka.
- Ayyukan Manzanni 24:18kusan 60 M.
Ni tsarkake ne sa’ad da suka same ni cikin filin haikalin ina yin haka. Babu taro tare da ni, ba kuwa ina tā da hankali ba.
- Ayyukan Manzanni 24:19kusan 60 M.
Amma akwai waɗansu Yahudawa daga lardin Asiya, waɗanda ya kamata suna a nan a gabanka su kawo ƙara in suna da wani a kaina.
- Ayyukan Manzanni 24:20kusan 60 M.
Ko kuwa waɗannan da suke a nan su faɗi laifin da suka same ni da shi sa’ad da na tsaya a gaban Majalisa,
- Ayyukan Manzanni 24:21kusan 60 M.
sai ko wannan abu ɗaya kaɗai da na ɗaga murya na faɗi yayinda nake tsaye a gabansu cewa, ‘A game da tashin matattu ake mini shari’a a gabanku yau.’ ”
- Ayyukan Manzanni 24:22kusan 60 M.
Sai Felis, wanda yake da cikakken sani game da Hanyar, ya ɗaga sauraron ƙarar. Ya ce, “In Lisiyas shugaban ƙungiyar soja ya iso, zan yanke muku shari’a.”
- Ayyukan Manzanni 24:23kusan 60 M.
Ya yi wa jarumin umarni yă tsare Bulus amma yă ba shi ’yanci yă kuma bar abokansa su lura da bukatunsa.
- Ayyukan Manzanni 24:24kusan 60 M.
Bayan ’yan kwanaki da dama sai Felis ya zo da matarsa Durusilla, mutuniyar Yahuda. Sai ya aika a zo da Bulus ya kuma saurare shi da yake magana game da bangaskiya cikin Kiristi Yesu.
- Ayyukan Manzanni 24:25kusan 60 M.
Da Bulus ya ci gaba jawabi a kan adalci, kamunkai da kuma hukunci mai zuwa, sai Felis ya tsorata ya ce, “Yanzu kam, ya isa haka! Kana iya tafi. In na sami zarafi, zan kira ka.”
- Ayyukan Manzanni 24:26kusan 60 M.
A wani fanni yana sa rai cewa Bulus zai ba shi toshiyar baki, saboda haka ya yi ta aika a kira masa Bulus yă yi magana da shi.
- Ayyukan Manzanni 24:27kusan 60 M.
Da shekaru biyu suka wuce, sai Forsiyus Festus, ya gāji Felis, amma domin Felis ya so yă biya wa Yahudawa bukata, sai ya bar Bulus a kurkuku.
- Ayyukan Manzanni 25:1kusan 62 M.
Kwana uku bayan isowa a lardin, sai Festus ya haura daga Kaisariya zuwa Urushalima,
- Ayyukan Manzanni 25:2kusan 62 M.
inda manyan firistoci da shugabannin Yahudawa suka bayyana a gabansa suka kuma gabatar da ƙararsu a kan Bulus.