- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 25:3kusan 62 M.
Suka roƙi Festus a gaggauce a matsayin alfarma gare su, da yă sa a mai da Bulus Urushalima, gama sun ’yan kwanto su kashe shi a hanya.
- Ayyukan Manzanni 25:4kusan 62 M.
Festus ya amsa ya ce, “Bulus yana tsare a Kaisariya, ni da kaina kuma zan je can ba da daɗewa ba.
- Ayyukan Manzanni 25:5kusan 62 M.
Ku sa waɗansu daga cikin shugabanninku su tafi tare da ni su kawo ƙararsu a kan mutumin a can, in ya aikata wani laifi.”
- Ayyukan Manzanni 25:6kusan 62 M.
Bayan ya yi kwanaki takwas ko goma tare da su, sai ya gangara zuwa Kaisariya, kashegari kuma ya kira a yi zaman kotu ya kuma umarta a kawo Bulus a gabansa.
- Ayyukan Manzanni 25:7kusan 62 M.
Da Bulus ya bayyana, sai Yahudawan da suka gangaro daga Urushalima suka tsaya kewaye shi, suna kawo ƙarar masu tsanani da yawa a kansa, waɗanda ba su iya tabbatarwa ba.
- Ayyukan Manzanni 25:8kusan 62 M.
Sa’an nan Bulus ya kāre kansa ya ce, “Ban aikata wani laifi game da dokokin Yahudawa ko game da haikali ko kuma game da Kaisar ba.”
- Ayyukan Manzanni 25:9kusan 62 M.
Festus, da yake yana so yă yi wa Yahudawa alfarma, sai ya ce wa Bulus, “Ka yarda ka je Urushalima a yi maka shari’a a can a gabana a kan waɗannan zarge?”
- Ayyukan Manzanni 25:10kusan 62 M.
Bulus ya amsa ya ce, “Yanzu ina tsaye a gaban kotun Kaisar, inda ya kamata a yi mini shari’a. Ban yi wani laifi ga Yahudawa ba, kai da kanka ma ka san da haka sarai.
- Ayyukan Manzanni 25:11kusan 62 M.
In kuwa ina da wani laifin da ya isa kisa, ban ƙi in mutu ba. Amma in ƙarar da waɗannan Yahudawa suka kawo a kaina ba gaskiya ba ne, ba wanda yake da iko ya ba da ni a gare su. Na ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar!”
- Ayyukan Manzanni 25:12kusan 62 M.
Bayan Festus ya yi shawara da majalisarsa sai ya ce, “Ka ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar. To, ga Kaisar kuwa za ka tafi!”
- Ayyukan Manzanni 25:13kusan 62 M.
Bayan ’yan kwanaki sai Sarki Agiriffa da Bernis suka iso Kaisariya don su yi wa Festus gaisuwar bangirma.
- Ayyukan Manzanni 25:14kusan 62 M.
Da yake za su yi kwanaki da dama a can, sai Festus ya tattauna batun Bulus da sarki. Ya ce, “Akwai mutumin da Felis ya bari a daure.
- Ayyukan Manzanni 25:15kusan 62 M.
Sa’ad da na je Urushalima, manyan firistoci da dattawan Yahudawa suka kawo ƙara game da shi suka kuma nema a hukunta shi.
- Ayyukan Manzanni 25:16kusan 62 M.
“Na gaya musu cewa ba al’adar Romawa ba ce a hukunta mutum kafin ya fuskanci masu ƙararsa ya kuma sami damar kāre kansa game da ƙararsu.
- Ayyukan Manzanni 25:17kusan 62 M.
Da suka zo nan tare da ni, ban yi wani jinkiri ba, na kira zaman kotu kashegari kuma na umarta a kawo mutumin.
- Ayyukan Manzanni 25:18kusan 62 M.
Sa’ad da masu zarginsa suka tashi tsaye don su yi magana, ba su zarge shi da wani laifin da na yi tsammani ba.
- Ayyukan Manzanni 25:19kusan 62 M.
A maimako haka, sai suka kawo waɗansu ’yan maganganu game da addininsu da ba su yarda da shi ba da kuma game da wani Yesu da ya mutu wanda Bulus ya ce yana da rai.
- Ayyukan Manzanni 25:20kusan 62 M.
Na rasa yadda zan bincike irin abubuwan nan; saboda haka na yi tambaya ko zai yarda ya tafi Urushalima a yi masa shari’a a can game da waɗannan zargi.
- Ayyukan Manzanni 25:21kusan 62 M.
Da Bulus ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Babban Sarki sai na umarta a tsare shi har kafin in aika shi zuwa ga Kaisar.”
- Ayyukan Manzanni 25:22kusan 62 M.
Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Ni ma zan so in saurari mutumin da kaina.” Sai ya amsa ya ce, “Za ka kuwa ji shi gobe.”
- Ayyukan Manzanni 25:23kusan 62 M.
Kashegari Agiriffa da Bernis suka yi shiga irin ta sarauta suka shiga ɗakin jama’a tare da manyan sojoji da manyan mutanen birni. Da umarnin Festus, sai aka shigo da Bulus.
- Ayyukan Manzanni 25:24kusan 62 M.
Sai Festus ya ce, “Sarki Agiriffa, da kuma dukan waɗanda suke tare da mu, kun ga wannan mutum! Dukan jama’ar Yahudawa sun kawo mini kararsa a Urushalima da kuma a nan Kaisariya, suna kururuwa suna cewa bai kamata a bar shi da rai ba.
- Ayyukan Manzanni 25:25kusan 62 M.
Ban same shi da wani laifin da ya isa kisa ba, amma saboda ya ɗaukaka ƙararsa zuwa gaban Babban Sarki sai na yanke shawara in aika da shi Roma.
- Ayyukan Manzanni 25:26kusan 62 M.
Ba ni da wata tabbatacciyar maganar da zan rubuta wa Mai Girma game da shi. Saboda haka na kawo shi a gabanku duka, musamman a gabanka, Sarki Agiriffa, saboda a sakamakon wannan bincike zan iya samun abin da zan rubuta.
- Ayyukan Manzanni 25:27kusan 62 M.
Don a ganina wauta ce a aika da ɗan kurkuku ba tare da an nuna zargin da ake yi a kansa ba.”