- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 26:26kusan 62 M.
Sarki ya san waɗannan abubuwa, ina kuma iya yin magana da shi a sake. Na tabbata cewa ba ɗaya daga cikin waɗannan da ya kuɓuce saninsa, domin ba a ɓoye aka yi shi ba.
- Ayyukan Manzanni 26:27kusan 62 M.
Sarki Agiriffa ka gaskata da annabawa? Na san ka gaskata.”
- Ayyukan Manzanni 26:28kusan 62 M.
Sai Agiriffa ya ce wa Bulus, “Kana tsammani cewa a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kana so ka mai da ni Kirista?”
- Ayyukan Manzanni 26:29kusan 62 M.
Bulus ya amsa ya ce, “Ko a ɗan lokaci, ko a lokaci mai yawa, ina addu’a ga Allah cewa, ba kai kaɗai ba amma duk waɗanda suke saurare ni a yau su zama abin da nake, sai dai ban da sarƙoƙin nan.”
- Ayyukan Manzanni 26:30kusan 62 M.
Sai sarki ya tashi, haka kuma gwamna da Bernis da kuma waɗanda suke zaune tare da su.
- Ayyukan Manzanni 26:31kusan 62 M.
Suka bar ɗakin, kuma yayinda suke magana da juna, sai suka ce, “Wannan mutum ba ya yin kome da ya isa kisa ko dauri.”
- Ayyukan Manzanni 26:32kusan 62 M.
Sai Agiriffa ya ce wa Festus, “Da ba don wannan mutum ya ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba da an sake shi.”
- Ayyukan Manzanni 27:1kusan 62 M.
Sa’ad da aka yanke shawara cewa za mu tashi a jirgin ruwa zuwa Italiya, sai aka danƙa Bulus da waɗansu ’yan kurkuku a hannun wani jarumin mai suna Juliyos, wanda yake na Bataliyar Babban Sarki.
- Ayyukan Manzanni 27:2kusan 62 M.
Muka shiga jirgin ruwa daga Andiramitiyum wanda yake shirin tashi zuwa tasoshin da suke bakin tekun lardin Asiya, sai muka kama tafiya. Aristarkus, mutumin Makidoniya daga Tessalonika, yana tare da mu.
- Ayyukan Manzanni 27:3kusan 62 M.
Kashegari muka sauka a Sidon; Juliyos kuwa, cikin alheri ga Bulus, ya bar shi yă je wajen abokansa domin su biya masa bukatunsa.
- Ayyukan Manzanni 27:4kusan 62 M.
Daga can kuma muka sāke kama tafiya muka zaga ta bayan tsibirin Saifurus saboda iska tana gāba da mu.
- Ayyukan Manzanni 27:5kusan 62 M.
Sa’ad da muka ƙetare tekun da yake sassan gaɓar Silisiya da Famfiliya sai muka sauka a Mira ta Lisiya.
- Ayyukan Manzanni 27:6kusan 62 M.
A can jarumin ya sami wani jirgin ruwan Alekzandariyan da za shi Italiya sai ya sa mu a ciki.
- Ayyukan Manzanni 27:7kusan 62 M.
Tafiyar ta ɗauki kwanaki da yawa muna yi kaɗan-kaɗan da ƙyar muka iso kusa da gaɓar Kinidus. Da iskar ta hana mu ci gaba, sai muka bi ta bayan tsibirin Kirit ɗaura da Salmone.
- Ayyukan Manzanni 27:8kusan 62 M.
Muka ci gaba a gefen gaɓar da ƙyar har muka iso wani wurin da ake kira Kyakkyawan Mafaka, kusa da garin Laseya.
- Ayyukan Manzanni 27:9kusan 62 M.
An riga an ɓata lokaci da yawa, tafiya kuwa ta riga ta zama da hatsari domin a lokacin Azumi ya riga ta wuce. Saboda haka Bulus ya gargaɗe su,
- Ayyukan Manzanni 27:10kusan 62 M.
ya ce, “Mutane, ina gani tafiyarmu za tă zama da masifa ta kuma kawo babbar hasara ga jirgin ruwan da kaya, da kuma ga rayukanmu ma.”
- Ayyukan Manzanni 27:11kusan 62 M.
Amma jarumin, a maimakon ya saurari abin da Bulus ya ce, sai ya bi shawarar matuƙi da kuma mai jirgin ruwan.
- Ayyukan Manzanni 27:12kusan 62 M.
Da yake tashar jirgin ruwan ba tă dace a ci damina a can ba, yawanci suka ba yanke shawara cewa mu ci gaba da tafiya, da bege za mu kai Funis mu ci damina a can. Wannan tashar jirgin ruwa ne a Kirit, tana fuskantar kudu maso yamma da kuma arewa maso yamma.
- Ayyukan Manzanni 27:13kusan 62 M.
Da iska ta fara busowa daga kudu a hankali, sai suka yi tsammani sun sami abin da suke nema; saboda haka suka janye ƙugiyar jirgin ruwa suka bi ta gefen tsibirin Kirit.
- Ayyukan Manzanni 27:14kusan 62 M.
Ba a jima ba, sai ga wata guguwar iska mai ƙarfin da ake kira “’Yar arewa maso gabas,” ta buga daga tsibirin.
- Ayyukan Manzanni 27:15kusan 62 M.
Iskar ta ci ƙarfin jirgin ruwan har ya kāsa fuskantar iskar; saboda haka muka sallamar mata tă yi ta tura mu.
- Ayyukan Manzanni 27:16kusan 62 M.
Da muka bi ta bayan wani ɗan tsibirin da ake kira Kauda, da ƙyar muka jawo ɗan ƙaramin jirgin kusa da jirgin.
- Ayyukan Manzanni 27:17kusan 62 M.
Da mutanen suka jawo shi cikin babban jirgin ruwan, sai suka sa igiyoyi ta ƙarƙashin jirgin ruwan kanta don su ɗaɗɗaura shi. Don gudun kada a fyaɗa mu da yashin gaɓar Sirtis, sai suka saukar da ƙugiyar jirgin ruwan, suka bari aka yi ta tura jirgin haka.
- Ayyukan Manzanni 27:18kusan 62 M.
Haka muka yi ta shan bugun guguwar hadarin nan kashegari suka fara jajjefar da kayan da jirgin yake ɗauke da su a cikin teku.