- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 27:19kusan 62 M.
A rana ta uku, da hannuwansu suka jefar da kayan aikin jirgin ruwan a cikin teku.
- Ayyukan Manzanni 27:20kusan 62 M.
Da dai aka yi kwana da kwanaki ba a ga rana ko taurari ba guguwar iska kuma ta ci gaba da bugowa, a ƙarshe muka fid da zuciya za mu tsira.
- Ayyukan Manzanni 27:21kusan 62 M.
Bayan mutanen sun daɗe ba su ci abinci ba, Bulus ya miƙe tsaye a gabansu ya ce, “Mutane, da kun ji shawarata na kada ku tashi daga Kirit, da ba ku fāɗa wannan masifa da hasara ba.
- Ayyukan Manzanni 27:22kusan 62 M.
Amma yanzu ina ƙarfafa ku ku yi ƙarfin hali, domin ba ɗayanku da zai rasa ransa; jirgin ruwan ne kaɗai zai hallaka.
- Ayyukan Manzanni 27:23kusan 62 M.
Jiya da dare wani mala’ikan Allahn da nake nasa nake kuma bauta wa ya tsaya kusa da ni
- Ayyukan Manzanni 27:24kusan 62 M.
ya ce, ‘Kada ka ji tsoro, Bulus. Lalle za ka tsaya a gaban Kaisar a yi maka shari’a; Allah kuma cikin alherinsa ya ba ka dukan rayukan mutanen da suke tafiya tare da kai.’
- Ayyukan Manzanni 27:25kusan 62 M.
Saboda haka ku yi ƙarfin hali, ku jama’a, gama gaskata Allah a kan cewa yadda aka faɗa mini ɗin nan, haka zai faru.
- Ayyukan Manzanni 27:26kusan 62 M.
Duk da haka, dole a fyaɗa mu a wani tsibiri.”
- Ayyukan Manzanni 27:27kusan 62 M.
A dare na goma sha huɗu iska dai tana ta korarmu a Tekun Adiriyatik, wajen tsakar dare sai masu tuƙin jirgin suka zaci sun yi kusa da ƙasa.
- Ayyukan Manzanni 27:28kusan 62 M.
Sai suka gwada zurfin ruwan suka ga ya kai ƙafa ɗari da ashirin. Bayan ɗan lokaci kaɗan suka sāke gwadawa suka ga zurfin ya kai ƙafa tasa’in.
- Ayyukan Manzanni 27:29kusan 62 M.
Don gudun kada a fyaɗa mu a kan duwatsu, sai suka saki ƙugiyoyin jirgin guda huɗu daga bayan jirgin suka yi fata gari ya waye.
- Ayyukan Manzanni 27:30kusan 62 M.
Cikin ƙoƙarin tserewa daga jirgin, sai masu tuƙin jirgin suka saukar da ɗan ƙaramin jirgin ruwan cikin tekun, suka yi kamar za su saki waɗansu ƙugiyoyi daga sashen gaba na babban jirgin ne.
- Ayyukan Manzanni 27:31kusan 62 M.
Sai Bulus ya ce wa jarumin da kuma sojojin, “In mutanen nan ba su tsaya a cikin jirgin nan ba, ba za ku tsira ba.”
- Ayyukan Manzanni 27:32kusan 62 M.
Sai sojojin suka yayyanke igiyoyin da suke riƙe da ɗan ƙaramin jirgin, suka bar shi ya bi ruwa.
- Ayyukan Manzanni 27:33kusan 62 M.
Kafin gari ya waye Bulus ya roƙe su duka su ci abinci. Ya ce, “Kwana goma sha huɗu ke nan, kuna zama cikin zulumi kun kuma kasance ba abinci, ba ku ci kome ba.
- Ayyukan Manzanni 27:34kusan 62 M.
Ina roƙonku yanzu ku ci abinci. Kuna bukatarsa don ku rayu. Ba ɗayanku da zai rasa ko gashin kansa guda ɗaya.”
- Ayyukan Manzanni 27:35kusan 62 M.
Bayan da ya faɗi haka, sai ya ɗauki burodi ya yi godiya ga Allah a gabansu duka. Sa’an nan ya gutsuttsura ya fara ci.
- Ayyukan Manzanni 27:36kusan 62 M.
Dukansu kuwa suka sami ƙarfafawa, suka kuma ci abinci.
- Ayyukan Manzanni 27:37kusan 62 M.
Dukanmu a jirgin kuwa mutane 276 ne.
- Ayyukan Manzanni 27:38kusan 62 M.
Sa’ad da suka ci iyakar abin da suke so, sai suka rage nauyin jirgin ta wurin zubar da hatsin a cikin tekun.
- Ayyukan Manzanni 27:39kusan 62 M.
Da gari ya waye, ba su gane ƙasar da suke ba, amma suka ga wani lungu da gaci mai yashi, sai suka yanke shawara su kai jirgin can in za su iya.
- Ayyukan Manzanni 27:40kusan 62 M.
Da suka yanke ƙugiyoyin, sai suka bar su a cikin teku a lokaci guda kuma suka ɓalle maɗaurin abin juya jirgin. Sai suka tā da filafilan gaban jirgin daidai yadda iska za tă tura shi gaba, sa’an nan suka nufi gaci.
- Ayyukan Manzanni 27:41kusan 62 M.
Amma jirgin ruwan ya shiga yashi ya kafe. Kan jirgin ya shiga cikin yashin ya kāsa motsi, sai jirgin ya fara farfashewa ta baya saboda haukan raƙuman ruwa.
- Ayyukan Manzanni 27:42kusan 62 M.
Sojojin suka yi niyya su kakkashe ’yan kurkukun don hana waninsu yă yi iyo yă tsere.
- Ayyukan Manzanni 27:43kusan 62 M.
Amma jarumin ya so yă ceci ran Bulus, sai ya hana su aiwatar da niyyarsu. Ya kuma yi umarni duk waɗanda suka iya ruwa su fara fāɗawa zuwa gaci.