- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa AD 30–62
The Early Church
Pentecost ignites a movement; Peter, Paul, and countless others carry the gospel from Jerusalem to the ends of the earth.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Ayyukan Manzanni 27:44kusan 62 M.
Sauran kuma su bi katakai zuwa can ko kuma a kan tarkacen jirgin ruwan. Ta haka kowa ya kai bakin teku lafiya.
- Ayyukan Manzanni 28:1kusan 62 M.
Bayan da muka kai bakin tekun lafiya, sai muka tarar cewa sunan tsibirin Malta ne.
- Ayyukan Manzanni 28:2kusan 62 M.
Mutanen tsibirin kuwa suka nuna mana babban alheri. Suka hura wuta suka marabce mu duka saboda ana ruwan sama da kuma sanyi.
- Ayyukan Manzanni 28:3kusan 62 M.
Bulus ya tattara tarin itace, yayinda kuma yake sa itacen a wuta, sai maciji ya ɓullo saboda zafi, ya dāfe a hannunsa.
- Ayyukan Manzanni 28:4kusan 62 M.
Da mutanen tsibirin suka ga macijin yana lilo a hannunsa, sai suka ce wa juna “Lalle, wannan mutum mai kisankai ne; gama ko da yake ya tsira daga teku, Adalci bai bar shi ya rayu ba.”
- Ayyukan Manzanni 28:5kusan 62 M.
Amma Bulus ya karkaɗe macijin a cikin wuta, bai kuwa ji wani ciwo ba.
- Ayyukan Manzanni 28:6kusan 62 M.
Mutanen kuma suka yi zato zai kumbura ko kuma nan da nan zai fāɗi matacce, amma da aka daɗe ba su ga wani abu ya faru da shi ba, sai suka sāke ra’ayi suka ce shi wani allah ne.
- Ayyukan Manzanni 28:7kusan 62 M.
Akwai wani filin nan kusa wanda yake na Fubiliyus, babban shugaban tsibirin. Shi ne ya karɓe mu a gidansa da alheri ya kuma ciyar da mu har kwana uku.
- Ayyukan Manzanni 28:8kusan 62 M.
Mahaifinsa kuwa yana kwanciya a gado yana fama da zazzaɓi da atuni. Bulus ya shiga ciki don yă gan shi, bayan ya yi masa addu’a, sai ya ɗibiya masa hannuwa ya warkar da shi.
- Ayyukan Manzanni 28:9kusan 62 M.
Sa’ad da wannan ya faru, sauran marasa lafiya a tsibirin suka zo aka kuma warkar da su.
- Ayyukan Manzanni 28:10kusan 62 M.
Suka girmama mu ta kowane hali da muka shirya za mu tashi, sai suka ba mu abubuwan da muke bukata.
- Ayyukan Manzanni 28:11kusan 62 M.
Bayan wata uku sai muka tashi a wani jirgin ruwan da ya ci damina a tsibirin. Jirgin ruwa kuwa na Alekzandariya ne yana da siffar tagwayen allolin Kasto da Follus.
- Ayyukan Manzanni 28:12kusan 62 M.
Muka isa Sirakus a can muka yi kwana uku.
- Ayyukan Manzanni 28:13kusan 62 M.
Daga can muka tashi muka isa Regiyum. Kashegari iskar kudu ta taso, kashegari kuma muka kai Futeyoli.
- Ayyukan Manzanni 28:14kusan 62 M.
A can muka tarar da waɗansu ’yan’uwa waɗanda suka gayyaci mu mu yi mako ɗaya da su. Da haka dai muka kai Roma.
- Ayyukan Manzanni 28:15kusan 62 M.
’Yan’uwan da suke can sun sami labari cewa muna zuwa, sai suka tashi tun daga Kasuwar Affiyus da Masauƙi Uku don su tarye mu. Da ganin mutanen nan sai Bulus ya gode wa Allah ya kuma sami ƙarfafawa.
- Ayyukan Manzanni 28:16kusan 62 M.
Da muka isa Roma, sai aka yarda wa Bulus yă zauna shi kaɗai, tare da sojan da zai yi gadinsa.
- Ayyukan Manzanni 28:17kusan 62 M.
Bayan kwana uku sai ya kira taron shugabannin Yahudawa. Da suka taru, Bulus ya ce musu, “’Yan’uwana, ko da yake ban yi wa mutanenmu wani laifi ba ko kuma wani abu game da al’adun kakanninmu, aka kama ni a Urushalima aka kuma ba da ni ga Romawa.
- Ayyukan Manzanni 28:18kusan 62 M.
Suka tuhume ni suka kuma so su sake ni, domin ba a same ni da wani laifin da ya cancanci kisa ba.
- Ayyukan Manzanni 28:19kusan 62 M.
Amma da Yahudawa suka ƙi, sai ya zama mini dole in ɗaukaka ƙara zuwa gaban Kaisar ba don ina da wani zargin da zan kawo game da mutanena ba.
- Ayyukan Manzanni 28:20kusan 62 M.
Saboda wannan ne na nemi in gan ku in kuma yi magana da ku. Saboda begen Isra’ila ne, nake a daure da wannan sarƙa.”
- Ayyukan Manzanni 28:21kusan 62 M.
Suka amsa cewa, “Ba mu sami wani wasiƙa daga Yahudiya game da kai ba, kuma ba kowa daga cikin ’yan’uwan da suka zo daga can ya kawo wani labari ko ya faɗi wani mummuna abu game da kai.
- Ayyukan Manzanni 28:22kusan 62 M.
Amma muna so mu ji ra’ayinka, gama mun san cewa mutane ko’ina suna muguwar magana a kan wannan ɗarikar.”
- Ayyukan Manzanni 28:23kusan 62 M.
Suka shirya su sadu da Bulus wata rana, suka ma zo da yawa fiye da dā a wurin da Bulus yake zama. Daga safe har zuwa yamma ya yi ta yin musu bayani, ya kuma shaida musu mulkin Allah yana ƙoƙarin rinjayarsu game da Yesu daga Dokar Musa da kuma daga Annabawa.
- Ayyukan Manzanni 28:24kusan 62 M.
Waɗansu suka rinjayu da abin da ya faɗa, amma waɗansu suka ba su gaskata ba.