- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
circa 1406–1380 BC
Conquest of Canaan
Joshua leads Israel across the Jordan into the promised land, defeating the Canaanite kingdoms one by one.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Yoshuwa 12:22kusan 1450 K.H.
sarkin Kedesh, ɗaya sarkin Yokneyam a Karmel, ɗaya
- Yoshuwa 12:23kusan 1450 K.H.
sarkin Dor (A Nafot Dor), ɗaya sarkin Goyim a Gilgal, ɗaya
- Yoshuwa 12:24kusan 1450 K.H.
sarki Tirza, ɗaya. Duka-duka dai sarakuna talatin da ɗaya ne.
- Yoshuwa 13:1kusan 1444 K.H.
Sa’ad da Yoshuwa ya tsufa, Ubangiji ya ce masa, “Ka tsufa ƙwarai, ga shi kuma akwai sauran ƙasa mai fāɗi da ba ku riga kun mallaka ba.
- Yoshuwa 13:2kusan 1444 K.H.
“Ga ƙasar da ta rage, “dukan yankunan Filistiyawa da na Geshurawa.
- Yoshuwa 13:3kusan 1444 K.H.
Daga Kogin Shihor a gabashin Masar zuwa sashen Ekron a arewa, dukan wannan ƙasa ana lissafta ta a cikin ƙasar Kan’aniyawa, ko da yake tana a sashen da sarakuna biyar na Filistiyawa na Gaza, Ashdod, Ashkeloniyawa, Gat da Ekron; na Awwiyawa.
- Yoshuwa 13:4kusan 1444 K.H.
Daga wajen kudu kuma, dukan ƙasar Kan’aniyawa ce. Iyakarta a arewa ta fara daga Ara ta Sidoniyawa har zuwa Afek, ta zarce har zuwa iyakar Amoriyawa;
- Yoshuwa 13:5kusan 1444 K.H.
da ƙasar Gebaliyawa; da dukan Lebanon wajen gabas daga Ba’al-Gad a gindin Dutsen Hermon zuwa Lebo Hamat.
- Yoshuwa 13:6kusan 1444 K.H.
“Dukan mazauna kan yankunan tuddai daga Lebanon zuwa Misrefot Mayim, wato, dukan Sidoniyawa, ni da kaina zan kore su a gaban Isra’ilawa. Ka tabbata ka raba wa Isra’ilawa ƙasar ta zama gādonsu kamar yadda na umarce ka,
- Yoshuwa 13:7kusan 1444 K.H.
ka raba ta tă zama gādo wa kabilu tara da kuma rabin kabilar Manasse.”
- Yoshuwa 13:8kusan 1444 K.H.
Rabin kabilar Manasse, mutanen Ruben da mutanen Gad suka karɓi rabonsu na gādo wanda Musa ya ba su a gabashin Urdun. Abin da Musa bawan Ubangiji ya ba su ke nan.
- Yoshuwa 13:9kusan 1444 K.H.
Wannan ya tashi daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, ya kuma haɗa da ƙasar da take tudun Medeba har zuwa Dibon,
- Yoshuwa 13:10kusan 1444 K.H.
da dukan garuruwan Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulkin Heshbon, har zuwa iyakar Ammonawa.
- Yoshuwa 13:11kusan 1444 K.H.
Haɗe da Gileyad, inda mutanen Geshur da Ma’aka suke. Dukan Dutsen Hermon, da dukan Bashan har zuwa Saleka,
- Yoshuwa 13:12kusan 1444 K.H.
wato, dukan masarautar Og a Bashan, wanda ya yi mulkin Ashtarot da Edireyi, yana cikin waɗanda suke na ƙarshe da ba a kashe ba a cikin Refahiyawa. Musa ya ci su da yaƙi, ya ƙwace ƙasarsu.
- Yoshuwa 13:13kusan 1444 K.H.
Amma Isra’ilawa ba su kori mutanen Geshur da Ma’aka ba, saboda haka suka ci gaba da zama cikin Isra’ilawa har wa yau.
- Yoshuwa 13:14kusan 1444 K.H.
Kabilar Lawiyawa ne kaɗai Musa bai ba ta gādo ba, gama hadayun ƙonawa da ake miƙa wa Ubangiji, Allah na Isra’ila ne gādonsu, kamar yadda ya yi musu alkawari.
- Yoshuwa 13:15kusan 1444 K.H.
Ga abin da Musa ya ba kabilar Ruben bisa ga iyalansu.
- Yoshuwa 13:16kusan 1444 K.H.
Abin da ya kama daga Arower a gefen kwarin Arnon, da kuma daga garin da yake tsakiyar kwarin, da dukan ƙasar tudu kusa da Medeba
- Yoshuwa 13:17kusan 1444 K.H.
zuwa Heshbon, da dukan garuruwan kan tudu, haɗe da Dibon, Bamot Ba’al, Bet-Ba’al-Meyon,
- Yoshuwa 13:18kusan 1444 K.H.
Yahza, Kedemot, Mefa’at,
- Yoshuwa 13:19kusan 1444 K.H.
Kiriyatayim, Sibma, Zeret Shahar kan tudu cikin kwari,
- Yoshuwa 13:20kusan 1444 K.H.
Bet-Feyor, gangaren Fisga da Bet-Yeshimot,
- Yoshuwa 13:21kusan 1444 K.H.
dukan garuruwan da suke kan tudu da dukan masarautar Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Musa ya yi nasara da shi, da shugabannin Midiyawa, wato, Ewi, Rekem, Zur, Hur, da Reba, sarakunan Sihon, waɗanda suka zauna a ƙasar.
- Yoshuwa 13:22kusan 1444 K.H.
Ƙari a kan waɗanda aka kashe a yaƙi, Isra’ilawa suka kashe Bala’am ɗan Beyor da takobi don yana duba.