Tsallake zuwa abun ciki

circa 1406–1380 BC

Conquest of Canaan

Joshua leads Israel across the Jordan into the promised land, defeating the Canaanite kingdoms one by one.

658 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Yoshuwa 24:26kusan 1427 K.H.

    Yoshuwa kuwa ya rubuta abubuwan nan a cikin Littafin Dokoki na Allah. Sa’an nan ya ɗauki babban dutse ya ajiye a ƙarƙashin itacen oak kusa da tsattsarkan wuri na Ubangiji.

  2. Yoshuwa 24:27kusan 1427 K.H.

    Ya ce wa duka mutanen, “Ku gani! Wannan dutse zai zama mana shaida, ya ji duk maganar da Ubangiji ya yi mana, zai zama muku shaida in ba ku yi wa Allahnku gaskiya ba.”

  3. Yoshuwa 24:28kusan 1427 K.H.

    Sai Yoshuwa ya sallami mutane, kowa ya tafi ƙasar da aka ba shi gādo.

  4. Yoshuwa 24:29kusan 1427 K.H.

    Bayan waɗannan abubuwa, Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekaru ɗari da goma.

  5. Yoshuwa 24:30kusan 1427 K.H.

    Suka kuma binne shi a ƙasarsa ta gādo, a Timnat Sera a ƙasar kan tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.

  6. Yoshuwa 24:31kusan 1427 K.H.

    Isra’ilawa kuwa sun bauta wa Ubangiji dukan kwanakin Yoshuwa, da kuma kwanakin dattawan da ya bari, da waɗanda suka ga duk abin da Ubangiji ya yi wa Isra’ila.

  7. Yoshuwa 24:32kusan 1427 K.H.

    Aka kuma binne ƙasusuwan Yusuf da aka kawo daga Masar, a Shekem a wurin da Yaƙub ya saya da azurfa ɗari daga ’ya’yan Hamor, babban Shekem. Wurin ya zama gādon zuriyar Yusuf.

  8. Yoshuwa 24:33kusan 1427 K.H.

    Eleyazar ɗan Haruna, ya mutu aka binne shi a Gibeya, wurin da aka ba ɗansa Finehas a ƙasar kan tudu ta Efraim.