Tsallake zuwa abun ciki

circa 1406–1380 BC

Conquest of Canaan

Joshua leads Israel across the Jordan into the promised land, defeating the Canaanite kingdoms one by one.

658 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Yoshuwa 11:20kusan 1450 K.H.

    Gama Ubangiji ne ya taurare zukatansu waɗannan sarakuna suka yi yaƙi da Isra’ilawa don yă hallaka su gaba ɗaya, yă gamar da su ba jinƙai, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  2. Yoshuwa 11:21kusan 1450 K.H.

    A lokacin nan Yoshuwa ya je ya hallaka Anakawa daga ƙasar tudu. Daga Hebron, Debir da Anab. Daga dukan ƙasar tuddai na Yahuda, da kuma dukan ƙasar tudu ta Isra’ila, Yoshuwa ya hallaka su duka da garuruwansu.

  3. Yoshuwa 11:22kusan 1450 K.H.

    Ba a bar waɗansu Anakawa a harabar Isra’ila ba; sai dai a Gaza, Gat da Ashdod ne aka samu waɗanda suka ragu da rai.

  4. Yoshuwa 11:23kusan 1450 K.H.

    Yoshuwa kuwa ya ƙwace dukan ƙasar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ya ba da ita ta zama ƙasar gādo ga Isra’ilawa, kabila-kabila. Ta haka ƙasar ta huta daga yaƙi.

  5. Yoshuwa 12:1kusan 1450 K.H.

    Waɗannan su ne sarakunan ƙasashen da Isra’ilawa suka ci da yaƙi, suka kuma mallaki ƙasarsu a gabashin Urdun, daga kwarin Arnon zuwa Dutsen Hermon haɗe da dukan gefen gabas na Araba.

  6. Yoshuwa 12:2kusan 1450 K.H.

    Sihon sarkin Amoriyawa, wanda ya yi mulki a Heshbon. Ya yi mulki daga Arower wadda take iyakar kwarin Arnon, daga tsakiyar kwarin har zuwa, Kogin Yabbok, wanda yake iyakar Ammonawa. Wannan ya haɗa da rabin Gileyad.

  7. Yoshuwa 12:3kusan 1450 K.H.

    Ya kuma yi mulki a kan gabashin Araba daga tekun Kinneret zuwa Tekun Araba (wato, Tekun Gishiri), zuwa Bet-Yeshimot da kuma kudu zuwa gangaren dutsen Fisga.

  8. Yoshuwa 12:4kusan 1450 K.H.

    Haka ma suka ci sashen Og sarkin Bashan, ɗaya daga cikin Refahiyawa na ƙarshe da ya yi mulki a Ashtarot da Edireyi.

  9. Yoshuwa 12:5kusan 1450 K.H.

    Mulkinsa ya taso daga Dutsen Hermon, da Saleka, da dukan Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma’akatiyawa haɗe da rabin Gileyad, zuwa kan iyakar Heshbon ta sarki Sihon.

  10. Yoshuwa 12:6kusan 1450 K.H.

    Sai Musa, bawan Ubangiji da Isra’ilawa suka ci Sihon da Og da yaƙi. Musa bawan Ubangiji kuwa ya ba da ƙasarsu ga mutanen Ruben, mutanen Gad da kuma rabin mutanen kabilar Manasse.

  11. Yoshuwa 12:7kusan 1450 K.H.

    Waɗannan su ne sarakuna da kuma ƙasashen da Yoshuwa da Isra’ilawa suka ci da yaƙi a yammancin Urdun, daga Ba’al-Gad a Kwarin Lebanon zuwa Dutsen Halak wanda ya miƙe zuwa Seyir. Yoshuwa ya raba ƙasarsu ta zama gādo ga Isra’ilawa bisa ga yadda aka raba su kabila-kabila.

  12. Yoshuwa 12:8kusan 1450 K.H.

    Ƙasar ta haɗa da ƙasar kan tudu, filayen arewanci, Araba, gangaren Dutse, da jejin, da kuma Negeb, wato, ƙasashen Hittiyawa, Amoriyawa, Kan’aniyawa, Ferizziyawa, Hiwiyawa, da Yebusiyawa.

  13. Yoshuwa 12:9kusan 1450 K.H.

    Sarkin Yeriko, ɗaya sarkin Ai (kusa da Betel), ɗaya

  14. Yoshuwa 12:10kusan 1450 K.H.

    sarkin Urushalima, ɗaya sarkin Hebron, ɗaya

  15. Yoshuwa 12:11kusan 1450 K.H.

    sarkin Yarmut, ɗaya sarkin Lakish, ɗaya

  16. Yoshuwa 12:12kusan 1450 K.H.

    sarkin Eglon, ɗaya sarkin Gezer, ɗaya

  17. Yoshuwa 12:13kusan 1450 K.H.

    sarkin Debir, ɗaya sarkin Bet-Gader, ɗaya

  18. Yoshuwa 12:14kusan 1450 K.H.

    sarkin Horma, ɗaya sarkin Arad, ɗaya

  19. Yoshuwa 12:15kusan 1450 K.H.

    sarkin Libna, ɗaya sarkin Adullam, ɗaya

  20. Yoshuwa 12:16kusan 1450 K.H.

    sarkin Makkeda, ɗaya sarkin Betel, ɗaya

  21. Yoshuwa 12:17kusan 1450 K.H.

    sarkin Taffuwa, ɗaya sarkin Hefer, ɗaya

  22. Yoshuwa 12:18kusan 1450 K.H.

    sarkin Afek, ɗaya sarkin Sharon, ɗaya

  23. Yoshuwa 12:19kusan 1450 K.H.

    sarkin Madon, ɗaya sarkin Hazor, ɗaya

  24. Yoshuwa 12:20kusan 1450 K.H.

    sarkin Shimron Meron, ɗaya sarkin Akshaf, ɗaya

  25. Yoshuwa 12:21kusan 1450 K.H.

    sarkin Ta’anak, ɗaya sarkin Megiddo, ɗaya