Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Woman

193 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya.

  2. Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.

  3. Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”

  4. A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,

  5. ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu,

  6. kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu,

  7. da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu,

  8. tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu

  9. da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale.

  10. A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana.

  11. A wannan rana mata guda bakwai za su cafke namiji guda su ce, “Ma ciyar da kanmu mu kuma yi wa kanmu sutura; ka dai bari mu ce kai ne mijinmu. Ka ɗauke mana kunyar da za mu sha.”

  12. Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za tă yi ciki, za tă haifi ɗa, za tă kuwa kira shi Immanuwel.

  13. A wannan rana Masarawa za su zama kamar mata. Za su yi rawar jiki lokacin da Ubangiji Maɗaukaki ya ɗaga hannu a kansu.

  14. Ku matan da kuke zaman jin daɗi, ku tashi ku saurare ni; ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya, ku ji abin da zan faɗa!

  15. Cikin ɗan lokaci ƙasa da shekara guda ku da kuke tsammani kuna da kāriya za ku yi rawar jiki; girbin ’ya’yan inabi zai kāsa, girbin ’ya’yan itatuwa kuma ba zai zo ba.

  16. Ku yi rawar jiki, ku mata masu jin daɗi, ku sha wahala, ku ’yan matan da kuke tsammani kuna da kāriya! Ku tuɓe rigunanku, ku ɗaura tsummoki a kwankwasonku.

  17. “Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa? Mai yiwuwa ta manta, amma ba zan taɓa manta da ke ba!

  18. Ubangiji zai kira sai ka ce ke mace ce da aka yashe ta tana kuma damuwa a ranta, macen da ta yi aure a ƙuruciya, sai kawai aka ƙi ta,” in ji Allahnki.

  19. Budurwa za tă manta da kayan adonta amarya ta manta da kayan adon aurenta? Duk da haka mutanena sun manta da ni, kwanaki ba iyaka.

  20. Zan hallaka Diyar Sihiyona, kyakkyawa da kuma mai laulayi.

  21. Yara sukan tara itace, iyaye suka hura wuta, mata kuma sukan kwaɓa kullu don su yi wa Sarauniyar Sama waina. Sukan miƙa hadayun sha ga waɗansu alloli don su tsokane ni in yi fushi.

  22. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku lura yanzu! Ku kira mata masu makoki su zo ku aika wa gwanaye a cikinsu su zo.

  23. Yanzu, ya mata, ku ji maganar Ubangiji; ku buɗe kunnuwanku ga maganar bakina. Ku koya wa ’yan matanku yadda za su yi kuka; ku koya wa juna makoki.

  24. ’Yan mata za su yi rawa su kuma yi murna, haka ma samari da tsofaffi. Zan mai da makokinsu farin ciki; zan ta’azantar da su in kuma sa su yi farin ciki a maimakon baƙin ciki.

  25. Akwai takobi a kan dawakanta da kekunan yaƙinta da kuma dukan baƙin da suke cikin mayaƙanta! Za su zama mata. Akwai takobi a kan dukiyarta! Za a washe su.