Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Woman: Deceived by Satan

8 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Deceived by Satan

  1. To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”

  2. Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun,

  3. amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”

  4. Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba.

  5. Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”

  6. Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci.

  7. Sai dai ina tsoro kada yă zama, kamar yadda maciji ya yaudari Hawwa’u da makircinsa, ku ma a bauɗar da hankalinku daga sahihiyar biyayya amintacciya ga Kiristi.

  8. Ba kuma Adamu ne aka yaudara ba; macen ce aka yaudara ta kuma zama mai zunubi.