Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Woman: Punishment for injuring, when with child

4 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Punishment for injuring, when with child

  1. “Idan mutum biyu suna faɗa, har suka yi wa mace mai ciki rauni, har ya sa ta yi ɓari, amma wani lahani bai same ta ba, za a ci wa wanda ya yi mata raunin tara bisa ga yadda mijinta ya yanka za a biya, in dai abin da ya yanka ya yi daidai da abin da alƙalai suka tsara.

  2. Amma in akwai rauni mai tsanani, sai a ɗauki rai a maimakon rai,

  3. ido don ido, haƙori don haƙori, hannu don hannu, ƙafa don ƙafa,

  4. ƙuna don ƙuna, rauni don rauni, ƙujewa don ƙujewa.