Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Woman: Drawing and carrying water

6 ayoyi · 73 fannoni

Ayoyi game da Drawing and carrying water

  1. Ya sa raƙuman suka durƙusa kusa da rijiya a bayan gari; wajen yamma ne, lokacin da mata sukan fita ɗiban ruwa.

  2. Duba, ina tsaye a bakin rijiyar ruwa, ’ya’ya matan mutanen gari kuma suna fitowa domin ɗiban ruwa.

  3. Kafin ya gama addu’a, sai Rebeka ta fito da tulu a kafaɗarta. Ita ’yar Betuwel ɗan Milka, matar Nahor, ɗan’uwan Ibrahim.

  4. Yarinyar kuwa kyakkyawa ce, budurwa, ba namijin da ya taɓa kwana da ita. Ta gangara zuwa rijiyar, ta cika tulunta ta kuma hauro.

  5. Sa’ad da suke haura tudun zuwa birnin, sai suka sadu da waɗansu ’yan mata sun fito za su ɗiban ruwa. Sai suka tambaye su, suka ce, “Mai duba yana nan?”

  6. Sa’ad da wata mutuniyar Samariya ta zo ɗiban ruwa, sai Yesu ya ce mata, “Ba ni ruwa in sha?”