Skip to content

Mizpah

6 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Mizpeh

32.5600, 36.0000 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Mizpah

  1. Aka kuma kira shi Mizfa, domin ya ce, “Ubangiji yă sa ido tsakanin ni da kai sa’ad da muka rabu da juna.

  2. Sa’ad da aka kira Ammonawa su yi ɗamarar yaƙi, sai su kuma kafa sansani a Gileyad, Isra’ilawa kuwa suka tattaru suka kafa sansani Mizfa.

  3. Saboda haka Yefta ya tafi tare da dattawan Gileyad, mutanen kuwa suka naɗa shi shugabansu da kuma sarkinsu. Ya kuwa maimaita dukan maganarsa a gaban Ubangiji a Mizfa.

  4. Sa’an nan Ruhun Ubangiji ya sauko wa Yefta. Sai ya haye Gileyad da Manasse, ya ratsa ta Mizfa zuwa Gileyad, daga can kuma ya kai wa Ammonawa hari.

  5. Sa’ad da Yefta ya komo gida a Mizfa, wa ya fito yă tarye shi, ’yarsa tilo, tana rawa kiɗin ganguna! Ita ce kaɗai ’yarsa. Ban da ita ba shi da ɗa ko ’ya.

  6. “Ku ji wannan, ku firistoci! Ku kasa kunne, ku Isra’ilawa! Ku saurara, ya ku gidan sarauta! Wannan hukunci yana a kanku, kun zama tarko a Mizfa, ragar da aka shimfiɗa a kan Tabor.