Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wives

73 ayoyi · 37 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Takan zaɓi ulu da lilin ta yi ta saƙa da hannuwanta da farin ciki.

  2. Ita kamar jirgin ’yan kasuwa ne tana kawo abincinta daga nesa.

  3. Takan farka tun da sauran duhu; ta tanada wa iyalinta abinci ta kuma shirya wa ’yan matan gidanta ayyukan da za su yi.

  4. Takan lura da gona sosai ta kuma saye ta; daga abin da take samu na kuɗin shiga take shuka gonar inabi.

  5. Takan himmantu tă yi aikinta tuƙuru; hannuwanta suna da ƙarfi domin ayyukanta.

  6. Takan tabbata akwai riba a kasuwancinta, kuma fitilarta ba ya mutuwa da dare.

  7. Da hannunta take riƙe abin kaɗi ta kuma kama abin saƙa da yatsotsinta.

  8. Takan marabci talakawa takan kuma taimaki masu bukata.

  9. Sa’ad da ƙanƙara ta fāɗi, ba ta jin tsoro saboda gidanta; gama dukansu suna da tufafi masu kauri.

  10. Takan yi wa gadonta kayan shimfiɗa; tufafinta kuma na lilin ne mai laushi na shunayya.

  11. Ana girmama mijinta a ƙofar shiga birni inda yakan zauna a cikin dattawan gari.

  12. Takan yi riguna na lilin ta sayar; takan kuma sayar wa ’yan kasuwa da ɗamara.

  13. Ƙarfi da mutunci su ne suturarta; za tă iya yin dariyar kwanaki masu zuwa.

  14. Tana magana da hikima, kuma umarnai mai aminci yana a harshenta.

  15. Tana lura da sha’anin gidanta kuma ba ta cin abincin ƙyuya.

  16. ’Ya’yanta sukan tashi su ce da ita mai albarka; haka mijinta ma, yakan kuma yabe ta yana cewa,

  17. Gama Hiridus da kansa ya ba da umarni a kama Yohanna, ya kuma sa aka daure shi, aka sa shi a kurkuku. Ya yi haka saboda Hiridiyas, matar ɗan’uwansa Filibus, wadda ya aura.

  18. Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.

  19. To wani mutum mai suna Ananiyas tare da matarsa Saffiratu, shi ma ya sayar da wata mallakarsa.

  20. Da cikakken sanin matarsa ya ajiye sashi daga cikin kuɗin don kansa, ya kuma kawo sauran ya ajiye a sawun manzanni.

  21. A can ya sadu da wani mutumin Yahuda mai suna Akwila, ɗan garin Fontus, wanda ya je can ba da daɗewa ba daga Italiya tare da matarsa Firiskila, gama Kalaudiyus ya umarci dukan Yahudawa su bar Roma. Sai Bulus ya tafi yă gan su,

  22. Sai ya fara magana gabagadi a majami’a. Sa’ad da Firiskila da Akwila suka ji shi, sai suka gayyace shi gidansu suka ƙara bayyana masa hanyar Allah sosai.

  23. Misali, bisa ga doka mace mai aure tana daure ga mijinta muddin mijin yana da rai, amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga dokar aure.

  24. Saboda haka fa, in ta auri wani yayinda mijinta yana raye, za a ce da ita mazinaciya. Amma in mijinta ya mutu, an sake ta ke nan daga wannan doka, ita kuwa ba mazinaciya ba ce, ko da yake ta auri wani.

  25. Ya kamata miji yă cika hakkinsa na aure ga matarsa. Haka kuma matar ta yi ga mijinta.