Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ceto yana nesa da mugaye, gama ba sa neman ƙa’idodinka.

  2. Amma waɗanda suka juye ga karkatattun hanyoyi Ubangiji zai kore su tare da masu aikata mugunta. Salama tă kasance tare da Isra’ila.

  3. Amma da yake kun ƙi ni sa’ad da na yi kira ba kuma wanda ya saurara sa’ad da na miƙa hannuna,

  4. da yake kun ƙi dukan shawarata ba ku kuma yarda da tsawatata ba,

  5. Zan yi muku dariya sa’ad da masifa ta same ku, zan yi muku ba’a sa’ad da bala’i ya same ku,

  6. sa’ad da bala’i ya sha kanku kamar hadiri, sa’ad da masifa ta share ku kamar guguwa, sa’ad damuwa da wahala suka mamaye ku.

  7. “Sa’an nan za su kira gare ni amma ba zan amsa ba; za su neme ni amma ba za su same ni ba.

  8. Da yake sun ƙi sani ba su kuwa zaɓi tsoron Ubangiji ba,

  9. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  10. Hikima za tă cece ka daga hanyoyin mugayen mutane, daga kalmomin mutane masu ɓatanci,

  11. waɗanda suke barin miƙaƙƙun hanyoyi don su yi tafiya a hanyoyi masu duhu,

  12. waɗanda suke jin daɗin yin abin da ba shi da kyau suna kuma farin ciki a mugayen ɓatanci,

  13. waɗanda hanyoyinsu karkatattu ne waɗanda kuma suke cuku-cuku a hanyoyinsu.

  14. Zai kiyaye ku kuma daga mazinaciya, daga mace mai lalata, mai ƙoƙarin kama ka da daɗin bakinta,

  15. wadda ta bar mijin ƙuruciyarta ta kuma ƙyale alkawarin da ta yi a gaban Allah.

  16. Gama gidanta yana kai ga mutuwa hanyarta kuma ga ruhohin matattu.

  17. Duk wanda ya ziyarce ta ba ya ƙara komowa ba zai ƙara komowa ga hanyar rai.

  18. Mugaye ba sa iya barci, sai sun aikata mugunta; ba su barci sai sun cuci wani.

  19. Sakare da mutumin banza wanda yana yawo da magana banza a baki,

  20. wanda yake ƙyifce da ido, yana yi alama da ƙafafunsa yana kuma nuni da yatsotsinsa,

  21. wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye

  22. Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.

  23. Albarka kan zauna a kan mai adalci kamar rawani, amma rikici kan sha bakin mugu.

  24. Mai mutunci yana tafiya lafiya, amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.

  25. Leɓunan adalai kan amfane yawanci, amma wawa kan mutu saboda rashin azanci.