Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Adali yakan yi hankali a abokantaka, amma hanyar mugaye kan kai su ga kaucewa.

  2. Adalci yakan lura da mutum mai mutunci, amma mugunta takan sha kan mai zunubi.

  3. Duk wanda ya rena umarni zai ɗanɗana ƙodarsa, amma duk wanda ya yi biyayya da umarni zai sami lada.

  4. Mugun ɗan saƙo kan shiga wahala, amma jakadan da mai aminci yakan kawo warkarwa.

  5. Marmarin da aka cika yana da daɗi ga rai, amma wawa yana ƙyamar juyewa daga mugunta.

  6. Rashin sa’a kan fafare mai zunubi, amma wadata ce ladar adali.

  7. Wawaye kan yi ba’a a gyaran zunubi, amma fatan alheri yana samuwa a cikin masu aikata gaskiya.

  8. Masu mugunta za su rusuna a gaban masu kirki, mugaye kuma za su yi haka a ƙofofin adalai.

  9. Ba waɗanda suke ƙulla mugunta sukan kauce ba? Amma waɗanda suke ƙulla abin da yake mai kyau sukan sami ƙauna da aminci.

  10. Sa’ad bala’i ya auku, mugaye kan fāɗi, amma ko a mutuwa masu adalci suna da mafaka.

  11. Gidan adali yana da dukiya mai yawa, amma albashin mugaye kan kawo musu wahala.

  12. Ubangiji yana ƙyamar hadayar mugaye, amma addu’ar masu aikata gaskiya kan sa ya ji daɗi.

  13. Ubangiji yana ƙin hanyar mugaye amma yana ƙaunar waɗanda suke neman adalci.

  14. Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu.

  15. Ubangiji yana nesa da mugaye amma yakan ji addu’ar adalai.

  16. In mutum ya toshe kunnuwansa ga kukan matalauci, shi ma zai yi kukan neman taimako ba kuwa zai sami amsa ba.

  17. Mugu kan zama abin fansa don adali, marar aminci kuma don mai aikata gaskiya.

  18. Dukan yini yana marmari ya sami ƙari, amma mai adalci yakan bayar hannu sake.

  19. Hadayar mugaye abin ƙyama ne, balle ma in aka kawo da mugun nufi!

  20. A hanyoyin mugu akwai kaya da tarko, amma duk wanda ya kiyaye ransa kan kauce musu.

  21. Ko da ka daka wawa a turmi, kana daka shi kamar hatsi da taɓarya, ba za ka fid da wauta daga gare shi ba.

  22. Mugu yakan gudu ko babu wanda yake korarsa, amma adalai suna da ƙarfin hali kamar zaki.

  23. Duk waɗanda ba sa bin doka yabon mugaye suke yi, amma waɗanda suke yin biyayya da doka suna gāba da mugaye ke nan.

  24. Mugaye ba su san gaskiya ba, amma waɗanda suke neman Ubangiji sun santa sosai.

  25. In wani ya yi kunnuwa ƙashi ga doka ko addu’arsa ma abar ƙyama ce.