Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara, amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

  2. Mai albarka ne mutumin da kullum yake jin tsoron Allah, amma duk wanda ya taurare zuciyarsa yakan shiga wahala.

  3. Duk wanda ya yi tafiya marar abin zargi zai zauna lafiya, amma duk wanda hanyoyinsa mugaye ne zai fāɗi nan da nan.

  4. Na sāke yin tunani, “Game da mutane kam, Allah kan gwada su don su san cewa ba su fi dabba ba.

  5. In ba a hanzarta aka yanke hukunci a kan laifi ba, zukatan mutane sukan cika da ƙulle-ƙullen aikata abubuwan da ba daidai ba.

  6. Ko da yake mugu ya aikata laifi ɗari ya kuma yi tsawon rai, na san cewa zai fi wa masu tsoron Allah kyau, waɗanda suke girmama Allah.

  7. Duk da haka, domin masu mugunta ba su ji tsoron Allah ba, abubuwa ba za su yi musu kyau ba, ransu kamar inuwa yake ba zai yi tsawo ba.

  8. Kash, ya ke al’umma mai zunubi, mutane cike da laifi, tarin masu aikata mugunta, ’ya’yan da aka miƙa wa lalaci! Sun yashe Ubangiji; sun rena Mai Tsarkin nan na Isra’ila suka juya masa baya.

  9. Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.

  10. Daga tafin ƙafarku zuwa saman kanku ba lafiya, sai miyaku da ƙujewa da manyan gyambuna, ba a tsabtacce su ba ko a daure ko shafa musu magani.

  11. Ku saurari maganar Ubangiji, ku masu mulkin Sodom; ku kasa kunne ga dokar Allahnmu, ku mutanen Gomorra!

  12. Ubangiji ya ce, “Yawan hadayunku, mene ne suke a gare ni?” Ina da isashen hadayun ƙonawa, na raguna da na kitsen dabbobi masu ƙiba; ba na jin daɗin jinin bijimai da na tumaki da kuma na awaki.

  13. Sa’ad da kuka zo don ku bayyana a gabana, wa ya nemi wannan daga gare ku, da kuke kai da kawowa a filayen gidana?

  14. Ku daina kawo hadayu marasa amfani! Turarenku abin ƙyama ne gare ni. Ina ƙin bukukkuwanku na Sabon Wata, da na ranakun Asabbaci, da taronku na addini, ba zan iya jure wa mugun taronku ba.

  15. Bukukkuwanku na Sabon Wata da na tsarkakan ranaku na ƙi su. Sun zama mini kaya; na gaji da ɗaukansu.

  16. Sa’ad da kuka ɗaga hannuwanku wajen yin addu’a, zan ɓoye fuskata daga gare ku; ko da kun miƙa addu’o’i masu yawa, ba zan kasa kunne ba. Hannuwanku sun cika da jini!

  17. Za ku zama kamar itacen oak mai busasshen ganyaye, kamar lambu marar ruwa.

  18. Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.

  19. Kaiton waɗanda suke tashi da sassafe don su nufi wurin shaye-shaye, waɗanda suke raba dare har sai sun bugu da ruwan inabi.

  20. Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu, ganguna da busa da ruwan inabi, amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba, ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.

  21. Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu, da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin,

  22. waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta, bari yă hanzarta aikinsa don mu gani. Bari yă iso, bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo, don mu sani.”

  23. Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagarta nagarta kuma mugunta, waɗanda suke mai da duhu haske haske kuma duhu, waɗanda suke mai da ɗaci zaƙi zaƙi kuma ɗaci.

  24. Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikima da kuma wayo a idonsu.

  25. Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabi da gwanaye a haɗin abubuwan sha,