Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da zuciyata ta ɓaci hankalina kuma ya tashi,

  2. na zama marar azanci da jahili; na zama kamar dabba a gabanka.

  3. Duk da haka kullum ina tare da kai; ka riƙe ni a hannun damana.

  4. Ka bishe ni da shawararka, bayan haka kuma za ka kai ni cikin ɗaukaka.

  5. Wa nake da shi a sama in ba kai ba? Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

  6. Jikina da zuciyata za su iya raunana, amma Allah ne ƙarfin zuciyata da kuma rabona har abada.

  7. Waɗanda suke nesa da kai za su hallaka; kakan hallaka dukan waɗanda suke maka rashin aminci.

  8. Amma game da ni, yana da kyau in kasance kusa da Allah. Na mai da Ubangiji Mai Iko Duka mafakata; zan yi shelar dukan ayyukanka.

  9. wanda ya ce, “Zan yanke ƙahonin dukan mugaye, amma za a ɗaga ƙahonin adalai sama.”

  10. Dubu za su iya fāɗuwa a gefenka, dubu goma a hannun damanka, amma ba abin da zai zo kusa da kai.

  11. Za ka dai gan da idanunka yadda ake hukunta mugaye.

  12. Mutum marar azanci ba zai sani ba, wawa ba zai gane ba,

  13. cewa ko da yake mugaye suna girma kamar ciyawa kuma dukan masu aikata mugunta suna haɓaka, za a hallaka su har abada.

  14. Har yaushe mugaye, ya Ubangiji har yaushe mugaye za su yi ta murna?

  15. Suna ta yin maganganun fariya; dukan masu aikata mugunta sun cika da fariya.

  16. Suna murƙushe mutanenka, ya Ubangiji; suna danne gādonka.

  17. Suna kashe gwauraye da kuma baƙi; suna kisan marayu.

  18. Suna ce, “Ubangiji ba ya gani; Allah na Yaƙub bai kula ba.”

  19. Ku mai da hankali, ku marasa azanci a cikin mutane; ku wawaye, yaushe za ku zama masu hikima?

  20. Ya mai da koguna suka zama hamada, maɓulɓulai masu gudu suka zama ƙasa mai ƙishirwa,

  21. ƙasa mai amfani kuma suka zama gishiri marar amfani, saboda muguntar waɗanda suka zauna a can.

  22. Ya mai da hamada ya zama tafkunan ruwa busasshiyar ƙasa kuma zuwa maɓulɓulai masu gudu;

  23. a can ya kai mayunwata su yi zama, ya kuma samo birnin da za su zauna.

  24. Suka yi shuka a gonaki suka dasa inabi suka kuma girbe amfani gona;

  25. ya albarkace su, yawansu kuma ya ƙaru, bai kuwa bar garkunansu suka ragu ba.