Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Unbelief

208 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ya zo wurin abin da yake nasa, amma nasa ɗin ba su karɓe shi ba.

  2. Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’

  3. Gaskiya nake faɗa maka, muna magana a kan abin da muka sani, muka kuma shaida abin da muka gani ne, amma har yanzu kun ƙi ku karɓi shaidarmu.

  4. Na yi muku magana a kan abubuwan duniya amma ba ku gaskata ba; to, yaya za ku gaskata in na yi magana a kan abubuwan sama?

  5. Duk wanda ya gaskata da shi ba za a yi masa hukunci ba, amma duk wanda bai gaskata ba an riga an yi masa hukunci domin bai gaskata da sunan wanda yake Ɗaya kuma Makaɗaicin Ɗan Allah ba.

  6. Yana ba da shaidar abin da ya gani da kuma ya ji, duk da haka ba wanda ya yarda da shaidarsa.

  7. Duk wanda ya gaskata da Ɗan yana da rai madawwami, amma duk wanda ya ƙi Ɗan ba zai sami rai ba, gama fushin Allah yana nan a bisansa.”

  8. Yesu ya ce masa, “Ku mutane, in ba kun ga alamu da abubuwan banmamaki ba, ba yadda za a yi ku ba da gaskiya.”

  9. maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba.

  10. duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.

  11. Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi.

  12. Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?

  13. Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni.

  14. Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”

  15. Amma kamar yadda na faɗa muku, kun gan ni duk da haka ba ku gaskata ba.

  16. Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan koyarwa tana da wuya. Wa zai iya yarda da ita?”

  17. Da yake ya san almajiransa suna gunaguni game da wannan, sai Yesu ya ce musu, “Wannan ya ɓata muku rai ne?

  18. Me za ku ce ke nan, in kuka gan Ɗan Mutum yana hawa zuwa inda yake dā!

  19. Duk da haka akwai waɗansunku da ba su gaskata ba.” Gama Yesu ya sani tun farko, waɗanda ba su gaskata ba, da kuma wanda zai bashe shi.

  20. Daga wannan lokaci da yawa daga cikin almajiransa suka ja da baya, suka daina bin sa.

  21. Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ba ni na zaɓe ku Sha Biyu ba? Amma ɗayanku Iblis ne!”

  22. (Yana nufin Yahuda, ɗan Siman Iskariyot, wanda, ko da yake ɗaya ne cikin Sha Biyun, zai bashe shi daga baya.)

  23. Domin ko ’yan’uwansa ma ba su gaskata da shi ba.

  24. Na gaya muku cewa za ku mutu cikin zunubanku; in ba ku gaskata cewa ni ne wanda na ce nake ba, lalle za ku mutu cikin zunubanku.”

  25. Amma domin ina faɗin gaskiya, ba kwa gaskata!