- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Unbelief: General references
Ayoyi game da General references
Musa ya amsa ya ce, “In ba su gaskata ni ba, suka kuma ce, ‘Ubangiji bai bayyana gare ka ba fa’?”
Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’
Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?”
Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.”
Amma Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna. “Tun da yake ba ku gaskata ni ba, ba ku kuwa ɗaukaka ni a idon Isra’ilawa ba, to, ba za ku kai taron jama’an nan a ƙasar da na ba su ba.”
Waɗannan su ne ruwan Meriba, inda Isra’ilawa suka yi wa Ubangiji gunaguni, inda kuma ya nuna kansa mai tsarki a cikinsu.
Suka yi magana a kan Allah, suna cewa, “Allah zai iya shimfiɗa tebur a cikin hamada?
Sa’ad da Ubangiji ya ji su, ya yi fushi ƙwarai; wutarsa ta ɓarke a kan Yaƙub, hasalarsa kuwa ta tashi a kan Isra’ila,
gama ba su gaskata ga Allah ba ko su dogara ga cetonsa.
Duk da haka, suka ci gaba da yin zunubi; duk da abubuwan banmamakinsa, ba su gaskata ba.
“Kada ku taurare zukatanku kamar yadda kuka yi a Meriba, kamar yadda kuka yi a wancan rana a Massa a hamada,
inda kakanninku suka gwada suka kuma jarraba ni, ko da yake sun ga abin da na yi.
Shekara arba’in na yi fushi da wancan tsara; na ce, ‘Su mutane ne waɗanda zukatansu suka kauce, kuma ba su san hanyoyina ba.’
Saboda haka na yi rantsuwa cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
Sa’ad da kakanninmu suke a Masar, ba su damu da mu’ujizanka ba; ba su tuna yawan alheranka ba, suka kuma yi tayarwa a teku, Jan Teku.
Sai suka rena ƙasa mai ni’ima; ba su gaskata alkawarinsa ba.
Ya ce, “Je ka ka faɗa wa wannan mutane, “ ‘Kome yawan kasa kunne da za ku yi, ba za ku fahimta ba; Kome yawan dubar da za ku yi, ba za ku san abin da yake faruwa ba.’
Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe; kunnuwansu su kurunce, idanunsu kuma su makance. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta da zuciyarsu, su kuma juyo a kuma warkar da su.”
Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ”
Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?
Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.
Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi.
Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.
Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.
Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”