Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Unbelief

208 ayoyi · 61 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ka sa zuciyar mutanen nan ta dushe; kunnuwansu su kurunce, idanunsu kuma su makance. In ba haka ba za su iya gani da idanunsu, su ji da kunnuwansu, su fahimta da zuciyarsu, su kuma juyo a kuma warkar da su.”

  2. Kan Efraim shi ne Samariya, kan Samariya kuma kawai shi ne ɗan Remaliya. In ba ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiyarku ba, ba za ku dawwama ba.’ ”

  3. Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?

  4. Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.

  5. Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi.

  6. Suna cewa, ‘Don me muka yi azumi, ba ka kuma gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, ba ka kuma lura da wannan ba?’ “Duk da haka a ranar azuminku, kuna yi yadda kuka ga dama kuna kuma zaluntar dukan ma’aikata.

  7. Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.

  8. Annabawa holoƙo ne kawai maganar kuwa ba ta cikinsu; saboda haka bari abin da suke faɗi ya koma kansu.”

  9. Saboda haka ga abin Ubangiji Allah Maɗaukaki yana cewa, “Domin mutanen sun yi waɗannan maganganu, zan mai da maganata a bakinku wuta waɗannan mutane kuwa su zama itacen da za tă ci.

  10. “Na ƙaunace ku, in ji Ubangiji. “Amma sai kuka ce, ‘Yaya ka ƙaunace mu?’ “Isuwa ba ɗan’uwan Yaƙub ba ne?” In ji Ubangiji. “Duk da haka na ƙaunaci Yaƙub,

  11. “Kun ajiye abinci mai ƙazanta a kan bagadena. “Sai kuka ce, ‘Yaya muka ƙazantar da kai?’ “Ta wurin cewa teburin Ubangiji abin reni ne.

  12. Duk wanda ya ƙi marabtarku ko ya ƙi sauraron kalmominku, sai ku karkaɗe ƙurar ƙafafunku sa’ad da kuka fita gidan ko garin.

  13. Gaskiya nake gaya muku, za a fi jin tausayin Sodom da Gomorra a ranar shari’a fiye da wannan gari.

  14. “Da me zan kwatanta wannan zamani? Suna kama da yara da suke zaune a kasuwa, suna kiran juna, suna cewa,

  15. “ ‘Mun yi muku busa, ba ku kuwa yi rawa ba, mun rera waƙar makoki, ba ku kuwa yi makoki ba.’

  16. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo ba ya ciye-ciye, ba ya shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ai, yana da aljani.’

  17. Ɗan Mutum ya zo yana ciye-ciye, yana shaye-shaye, sai suka ce, ‘Ga mai haɗama da kuma mashayi, abokin masu karɓar haraji da masu zunubi.’ Amma akan tabbatar da hikima ta wurin ayyukanta.”

  18. Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan. “Ko da yake suna kallo, ba sa gani; ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.

  19. A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa, “ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba; za ku yi ta kallo amma ba za ku taɓa gani ba.

  20. Gama zuciyar mutanen nan ta taurare; da ƙyar suke ji da kunnuwansu, sun kuma rufe idanunsu. Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu, su kuma ji da kunnuwansu, su gane a zuciyarsu, su kuwa juya, in kuma warkar da su.’

  21. Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

  22. Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurinkai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.”

  23. Sa’an nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”

  24. Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”

  25. Gama Yohanna Mai Baftisma ya zo wurinku don yă nuna muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba, amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata. Har ma bayan kun ga wannan, ba ku tuba kun gaskata shi ba.”