Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titles and Names of Ministers

54 ayoyi · 38 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. A maimakon haka, duk abin da muke yi, muna yin shi ne don mu nuna cewa mu masu hidimar Allah ne. Muna yin haka cikin jimrewa, da shan wahala, da shan wuya, har da shan masifu.

  2. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.

  3. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,

  4. Don haka, ba abin mamaki ba ne, in bayin Shaiɗan sun ɓad da kamanni kamar su bayin adalci ne. A ƙarshe, za a sāka musu gwargwadon ayyukansu.

  5. Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.

  6. Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai.

  7. Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, Zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima.

  8. Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.

  9. Sai ku ci gaba cikin bangaskiyarku, kuna tsaye a kafe kuma tsayayyu, ba tare da gusawa daga begen da kuka ji daga bishara ba. Wannan ita ce bisharar da kuka ji wadda aka yi shelarta ga kowace halittar da take ƙarƙashin sama, wadda kuma ni Bulus, na zama mai hidimarta.

  10. Yanzu, ina farin ciki saboda wuyar da nake sha dominku, don ta wurin wuyan nan zan cika abin da ya rage na wuyar da Kiristi ya sha saboda jikinsa, wato, ikkilisiya.

  11. Na zama mai hidimar ikkilisiya bisa ga aikin nan da Allah ya ba ni amana saboda ku, domin in sanar da maganar Allah sosai.

  12. Mun riga mun sha wahala, aka kuma zage mu a Filibbi, kamar yadda kuka sani, amma da taimakon Allahnmu muka yi ƙarfin hali muka sanar muku bishararsa duk da matsananciyar gāba.

  13. Don haka ne aka sa ni mai wa’azi, da manzo kuma, gaskiya nake faɗa, ba ƙarya ba, na kuma zama malami mai koya wa al’ummai al’amarin bangaskiya da kuma na gaskiya.

  14. Ga wata tabbatacciyar magana. In wani ya sa zuciyarsa a kan zama mai kula da ikkilisiya, yana marmarin yin aiki mai daraja ne.

  15. Haka masu hidima a cikin ikkilisiya; su ma, su zama maza da sun cancanci girmamawa, masu gaskiya, ba masu yawan shan ruwan inabi ba, ba masu kwaɗayin ƙazamar riba ba.

  16. Dattawan da suka bi da al’amuran ikkilisiya da kyau sun cancanci girmamawa ninki biyu, musamman waɗanda aikinsu wa’azi ne da kuma koyarwa.

  17. Ka jure wa shan wahala tare da mu kamar soja mai kyau na Kiristi Yesu.

  18. Bai kamata bawan Ubangiji yă zama mai neman faɗa ba; a maimako, dole yă nuna alheri ga kowa, mai iya koyarwa, mai haƙuri kuma.

  19. Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.

  20. Bulus, bawan Allah da kuma manzon Yesu Kiristi saboda bangaskiyar zaɓaɓɓu na Allah da kuma sanin gaskiya wadda take kaiwa ga rayuwa ta tsoron Allah

  21. Da yake an danƙa wa mai kula da ikkilisiya riƙon amana saboda Allah, dole yă zama marar aibi ba mai girman kai ba, ba mai saurin fushi ba, ba mai buguwa ba, ba mai rikici ba, ba kuma mai son ƙazamar riba ba.

  22. Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,

  23. Yaƙub, bawan Allah da kuma na Ubangiji Yesu Kiristi, Zuwa ga kabilan nan goma sha biyu, da suke warwartse a cikin al’ummai. Gaisuwa mai yawa.

  24. Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.

  25. Zuwa ga dattawan da suke cikinku, ina roƙo a matsayin ɗan’uwanku dattijo, mashaidin shan wahalar Kiristi wanda kuma shi ma zai sami rabo cikin ɗaukakar da za a bayyana.