Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titles and Names of Ministers

54 ayoyi · 38 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ko da yake Ubangiji yakan ba da abincin azaba da ruwan wahala, ba za a ƙara ɓoye malamanku ba; da idanunku za ku gan su.

  2. Na sa matsara a kan katangarki, ya Urushalima; ba za su taɓa yin shiru ba, dare da rana. Ku da kuke kira bisa sunan Ubangiji, kada ku ba kanku hutu,

  3. Sa’an nan zan ba ku makiyaya da suke yin abin da zuciyata take so, waɗanda za su bishe ku da sani da kuma fahimi.

  4. Zan sa makiyaya a kansu waɗanda za su lura da su, ba za su ƙara jin tsoro ko razana ba, ba kuwa waninsu da zai ɓace,” in ji Ubangiji.

  5. “Ɗan mutum, na mai da kai mai tsaro bisa gidan Isra’ila; saboda haka ka ji abin da zan faɗa ka kuma gargaɗe su.

  6. Zai zama tsattsarkan rabo na ƙasa domin firistoci, waɗanda za su yi hidima a cikin wuri mai tsarki da kuma waɗanda za su zo kusa don su yi hidima a gaban Ubangiji. Zai zama wuri don gidajensu ya kuma zama tsattsarkan wuri saboda wuri mai tsarki.

  7. Iri suna ta yanƙwanewa a busasshiyar ƙasa Ɗakunan ajiya sun lalace, an rurrushe rumbunan hatsin, gama hatsi ya ƙare.

  8. “Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki.

  9. Sai Yesu ya ce, “Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina.”

  10. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”

  11. Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”

  12. kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara.

  13. Da gari ya waye, sai ya kira almajiransa zuwa wurinsa, ya zaɓi guda goma sha biyu daga cikinsu, waɗanda ya kira su, Manzanni.

  14. Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya.”

  15. Mu shaidu ne ga waɗannan abubuwa, haka kuma Ruhu Mai Tsarki, wanda Allah ya ba wa waɗanda suke yin masa biyayya.”

  16. A waɗannan kwanaki, sa’ad da yawan almajirai suke ƙaruwa, sai Yahudawan masu jin Hellenanci a cikinsu suka yi gunaguni a kan Yahudawan da suke Ibraniyawa domin ba a kula da gwaurayensu a wajen raba abinci na yau da kullum.

  17. Ku lura da kanku da dukan garken da Ruhu Mai Tsarki ya sa ku ku zama masu kula da shi. Ku zama masu kiwon ikkilisiyar Allah, wadda ya saya da jininsa.

  18. Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.

  19. To, ta yaya za su kira ga wanda ba su gaskata ba? Ta yaya kuma za su gaskata wanda ba su taɓa ji ba? Ta yaya kuma za su ji ba tare da wani ya yi musu wa’azi ba?

  20. in zama mai hidimar Kiristi Yesu ga Al’ummai da aikin firist na yin shelar bisharar Allah, don Al’ummai su zama hadaya mai karɓuwa ga Allah, tsattsarka ta wurin Ruhu Mai Tsarki.

  21. Saboda haka, ya kamata mutane su ɗauke mu a matsayin bayin Kiristi, da kuma a matsayin waɗanda aka ba su amanar asirin abubuwan Allah.

  22. Shi ya sa muka gwaninta a matsayinmu na masu hidimar sabon alkawari ba ta rubutacciyar Dokar ba, amma ta Ruhu; don Dokar, kisa take yi, Ruhu kuwa yana ba da rai.

  23. Gama ba wa’azin kanmu muke yi ba, sai dai na Yesu Kiristi, a kan shi ne Ubangiji, mu kuma bayinku saboda Yesu.

  24. Saboda haka, mu jakadu ne na Kiristi, sai ka ce Allah kansa yake magana ta wurinmu. Muna roƙonku a madadin Kiristi. Ku sulhuntu da Allah.

  25. A matsayinmu na abokan aikin Allah, muna roƙonku kada ku karɓi alherin Allah a banza.