Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rebellion Against God

148 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. tawaye da mūsun Ubangiji, mun juye bayanmu ga Allahnmu, zugawa a yi zalunci da tayarwa, faɗin ƙarairayi da zukatanmu suka shirya.

  2. Duk da haka suka yi tawaye suka ɓata wa Ruhu Mai Tsarki rai. Saboda haka ya juya ya kuma zama abokin gābansu shi kansa kuma ya yaƙe su.

  3. Dukan yini ina miƙa hannuwana ga mutane masu tayarwa, waɗanda suna tafiya a hanyoyin da ba su da kyau, suna bin tunaninsu,

  4. “A faɗa wa al’ummai wannan, a furta wannan game Urushalima. ‘Sojoji masu ƙawanya suna zuwa daga ƙasa mai nisa, suna tā da kirarin yaƙi a kan biranen Yahuda.

  5. Sun kewaye ta kamar masu gadin fili, domin ta yi mini tawaye,’ ” in ji Ubangiji.

  6. “Halinki da ayyukanki sun kawo wannan a kanki. Hukuncinki ke nan. Yana da ɗaci! Ya soke ki har zuciyarki!”

  7. Amma mutanen nan suna da tauraren zukata, kuma ’yan tawaye ne; sun kauce suka kuma rabu da ni.

  8. Saboda haka, ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Ina shirin kawar da kai daga fuskar duniya. A wannan shekara za ka mutu, domin ka yi wa’azin tawaye a kan Ubangiji.’ ”

  9. “Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.

  10. “Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa.

  11. Ya ce, “Ɗan mutum, ina aikan ka zuwa ga Isra’ilawa, zuwa ga al’ummar ’yan tawayen nan da suka yi mini tayarwa; su da kakanninsu sun yi mini tawaye har yă zuwa yau.

  12. Mutanen da nake aikan ka masu ƙin ji ne da kuma taurinkai. Ka faɗa musu cewa, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya faɗa.’

  13. Kuma ko su ji ko kada su ji, gama su gida ne mai tawaye, za su san cewa akwai annabi a cikinsu.

  14. Kai kuwa, ɗan mutum, kada ka ji tsoro, ko da sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa duk sun kewaye ka kana kuma zama a cikin kunamai. Kada ka ji tsoron abin da za ka faɗa ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gida ne mai tawaye.

  15. Dole ka yi maganata gare su, ko su ji ko kada su ji, gama su ’yan tawaye ne.

  16. Amma kai, ɗan mutum, ka saurari abin da zan faɗa maka. Kada ka yi tawaye kamar wannan gidan ’yan tawaye; ka buɗe bakinka ka kuma ci abin da na ba ka.”

  17. Sa’an nan ya ce mini, “Ɗan mutum, yanzu ka tafi gidan Isra’ila ka faɗa kalmomina gare su.

  18. Ba ina aikan ka wurin mutanen da suke da baƙon harshe da kuma yare mai wuya ba ne, amma zuwa ga gidan Isra’ila ne,

  19. ba ga mutane da yawa na baƙon harshe da yare mai wuya, waɗanda ba ka san kalmominsu ba. Tabbatacce da na aike ka wurin irinsu, da sun saurare ka.

  20. Amma gidan Isra’ila ba sa niyya su saurare ka domin ba sa niyya su saurare ni, gama dukan gidan Isra’ila sun taurare suna kuma kin ji.

  21. Amma zan sa ka zama mai taurinkai da taurin zuciya kamar su.

  22. Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne.”

  23. “Ka faɗa wa gidan ’yan tawayen nan, ‘Ba ka san abin da waɗannan abubuwa suke nufi ba?’ Ka faɗa musu cewa, ‘Sarkin Babilon ya tafi Urushalima ya tafi da sarkinta da kuma manyan garinta, ya dawo da su Babilon.

  24. Amma sarkin nan ya yi tawaye a kan sarkin Babilon ta wurin aika jakadunsa zuwa Masar don a ba shi dawakai da sojoji masu yawa. Zai ci nasara? Shi da ya yi wannan abu zai tsira? Zai iya taka yarjejjeniya har ya tsere?

  25. “ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar.