Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rebellion Against God

148 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Daga bisani sai Musa da Haruna suka tafi wurin Fir’auna suka ce, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila ya ce, ‘Bari mutanena su tafi domin su yi mini biki a hamada.’ ”

  2. Fir’auna ya ce, “Wane ne Ubangiji da zan yi biyayya da shi, har in bar Isra’ila su tafi? Ban san Ubangiji ba, kuma ba zan bar Isra’ila su tafi ba.”

  3. “Ga shi, zan aika mala’ika a gabanku, yă tsare ku a tafiyarku, yă kuma kawo ku wurin da na shirya.

  4. Ku saurare shi, ku kuma kasa kunne ga abin da yake faɗa. Kada ku yi masa tawaye; ba zai gafarta tawayenku ba, gama shi wakilina ne.

  5. Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”

  6. Ubangiji ya ce wa Musa, “Na ga waɗannan mutane, mutane ne masu taurinkai.”

  7. “ ‘Amma in za ku kasa kunne gare ni, ku kuma aikata dukan waɗannan umarnai,

  8. in kuka kuma ƙi farillaina, kuka yi ƙyamar dokokina, kuka kuma kāsa kiyaye umarnaina, har kuka karya alkawarina,

  9. to, zan yi muku wannan. Zan kawo muku abin bantsoro, cututtuka da zazzaɓin da zai lalatar da idonku, yă kuma sa ranku a wahala. Za ku shuka iri a banza, domin abokan gābanku ne za su ci.

  10. Zan yi gāba da ku har abokan gābanku su ci ku a yaƙi, su waɗanda suke ƙinku za su yi mulki a kanku, za ku gudu ba tare da wani yana korinku ba.

  11. “ ‘In bayan dukan wannan, ba ku saurare ni ba, zan hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai.

  12. Zan karya ikonku wanda kuke fariya da shi, in hana ruwan sama, ƙasa kuma tă zama kamar tagulla.

  13. Ƙarfinku zai ƙare a banza domin ƙasarku ba za tă ba da hatsi ba, balle itatuwan ƙasar su ba da ’ya’ya.

  14. “ ‘In kuka ci gaba da tayar mini, kuka ƙi ku saurare ni, zan ninka wahalolinku sau bakwai, yadda ya dace da zunubanku.

  15. Zan aika da mugayen namun jeji a kanku, za su kuwa kashe ’ya’yanku, su hallaka shanunku, su rage yawanku, ku zama kaɗan. Wannan zai sa a rasa mutane a kan hanyoyinku.

  16. “ ‘In duk da waɗannan abubuwa, ba ku yarda da gyaran da nake yi muku ba, kuka ci gaba da yin adawa da ni,

  17. zan yi adawa da ku, zan kuma aukar muku saboda zunubanku har sau bakwai.

  18. Zan kawo takobi a kanku don in yi ramuwa saboda karya alkawarin da kuka yi. Sa’ad da kuka janye zuwa cikin biranenku, zan aika da annoba a cikinku, za a kuwa ba da ku ga hannun abokan gāba.

  19. Sa’ad da na yanke abincinku, mata goma za su dafa abinci a murhu ɗaya, za su kuma rarraba abincin a ma’auni. Za ku ci amma ba za ku ƙoshi ba.

  20. “ ‘In duk da haka kuka ci gaba da ƙin saurare ni, kuka ci gaba da yin adawa da ni,

  21. cikin fushina, sai in yi adawa da ku, in kuma hukunta ku saboda zunubanku har sau bakwai.

  22. Za ku ci naman ’ya’yanku maza da na ’ya’yanku mata.

  23. Zan rurrushe dukan masujadanku, in yanke bagadanku na turare, in yi tarin gawawwakinku a kan gumakanku, zan kuma yi ƙyamarku.

  24. Zan mai da biranenku kango, in lalace wuraren tsarkinku, ba zan kuma shaƙi ƙanshi hadayunku ba.

  25. Zan mai da ƙasarku kango har abokan gābanku da suke zama a wurin su yi mamaki.