Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Rebellion Against God: Refusing to hearken to him
Ayoyi game da Refusing to hearken to him
Sa’ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh Barneya ya ce, “Ku haura ku mallaki ƙasar da na ba ku.” Amma kuka yi tawaye ga umarnin Ubangiji Allahnku. Ba ku amince da shi, ko ku yi masa biyayya ba.
“ ‘Amma sai suka yi tawaye a kaina ba su kuwa saurare ni ba; ba su zubar da mugayen siffofin da suka kafa idanunsu a kai ba, balle su ƙi gumakan Masar. Saboda haka zan zubo hasalata a kansu in kuma aukar musu da fushina a Masar.
“Amma suka ƙi su saurara; da taurinkai suka juya bayansu suka kuma toshe kunnuwansu.