Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Paul

619 ayoyi · 103 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Sai na yi tambaya, na ce, ‘Me zan yi, ya Ubangiji?’ “Ubangiji ya ce, ‘Tashi, ka tafi cikin Damaskus. A can za a faɗa maka duk abin da aka shirya za ka yi.’

  2. Abokan tafiyata suka ja ni a hannu zuwa cikin Damaskus, saboda ƙarfin hasken ya makanta ni.

  3. “Wani mutumin da ake kira Ananiyas ya zo ya gan ni. Shi mai ibada ne wajen kiyaye dokoki wanda dukan Yahudawan da suke zama a can suna girmama shi ƙwarai.

  4. Ya tsaya kusa da ni ya ce, ‘Ɗan’uwa Shawulu, ka sami ganin garinka!’ A daidai lokacin kuwa na iya ganinsa.

  5. “Sa’an nan ya ce, ‘Allah na kakanninmu ya zaɓe ka ka san nufinsa ka kuma ga Mai Adalcin nan ka kuma ji kalmomi daga bakinsa.

  6. Za ka zama mai shaidarsa ga dukan mutane game da abin da ka gani ka kuma ji.

  7. Yanzu me kake jira? Ka tashi, a yi maka baftisma, a wanke zunubanka, ta wurin kira bisa ga sunansa.’

  8. “Sa’ad da na dawo Urushalima ina cikin addu’a a haikali, sai na ga wahayi

  9. na ga Ubangiji yana magana. Ya ce mini, ‘Maza! Ka bar Urushalima, gama ba za su yarda da shaidarka game da ni ba.’

  10. “Na amsa na ce, ‘Ubangiji, waɗannan mutane sun san cewa na bi majami’a-majami’a na jefa waɗanda suka gaskata da kai a cikin kurkuku, in kuma yin musu dūka.

  11. Sa’ad da kuma aka zub da jinin Istifanus mashaidinka, na tsaya can ina ba da goyon bayana ina kuma tsaron tufafin masu kisansa.’

  12. “Sa’an nan Ubangiji ya ce mini, ‘Je ka; zan aike ka can nesa a wurin Al’ummai.’ ”

  13. Taron suka saurari Bulus sai da ya yi wannan magana. Sa’an nan suka ɗaga muryoyinsu suka yi ihu suka ce, “A raba duniya da wannan mutum! Bai cancanci yă rayu ba!”

  14. Da suna ihu suna kaɗa mayafansu suna da tā da ƙura sama,

  15. sai shugaban ƙungiyar sojan ya umarta a kai Bulus a barikin soja. Ya ba da umarni a yi masa bulala a kuma tambaye shi abin da ya sa mutane suke masa ihu haka.

  16. Suna kwantar da shi ke nan domin a yi masa bulala, sai Bulus ya ce wa jarumin da yake tsaye a nan, “Ashe, daidai ne bisa ga doka a yi wa ɗan ƙasar Roma bulala wanda ba a ma tabbatar da laifi a kansa ba?”

  17. Da jarumin ya ji haka sai ya je wurin shugaban ƙungiyar sojan ya ce masa, “Me kake so yi ne? Wannan mutum ɗan ƙasar Roma ne.”

  18. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya je ya tambayi Bulus ya ce, “Faɗa mini, kai ɗan ƙasar Roma ne?” Bulus ya ce, “I.”

  19. Sai shugaban ƙungiyar sojan ya ce, “Sai da na biya kuɗi mai yawa kafin in zama ɗan ƙasa.” Bulus ya ce, “Ni kuwa an haife ni ɗan ƙasa.”

  20. Waɗanda dā suke shirin yin masa tambayoyi suka ja da baya nan da nan. Shugaban ƙungiyar sojan kansa ya tsorata da ya fahimci cewa ya sa wa Bulus, ɗan ƙasar Roma sarƙa.

  21. Kashegari da yake shugaban ƙungiyar sojan ya so yă tabbatar da ainihin abin da ya sa Yahudawa suke zargin Bulus, sai ya sake shi ya kuwa umarci manyan firistoci da dukan Majalisar su taru. Sa’an nan ya kawo Bulus ya sa ya tsaya a gabansu.

  22. Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.”

  23. Da jin wannan Ananiyas babban firist ya umarci waɗanda suke tsaye kusa da Bulus su buge bakinsa.

  24. Sai Bulus ya ce masa, “Allah zai buge ka, kai farin bango! Ka zauna a can kana hukunta ni bisa ga doka, ga shi kai kanka kana ƙetare dokar ta wurin ba da umarni a buge ni!”

  25. Waɗanda suke tsaye kusa da Bulus kuwa suka ce masa, “Babban firist na Allah za ka zaga?”