Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Malice

135 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yakan ragargaza waɗanda suka shiga hannu, su fāɗi; sukan fāɗi a ƙarƙashin ƙarfinsa.

  2. Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,

  3. “Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.”

  4. Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama.

  5. Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,

  6. nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.

  7. Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.

  8. Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya.

  9. Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina.

  10. Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.

  11. Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.”

  12. Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”

  13. Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.

  14. Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,

  15. “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”

  16. Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta.

  17. Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.

  18. Dukan yini sun yi ta juya maganata; kullum suna ƙulle-ƙulle su cuce ni.

  19. Sun haɗa baki, sun ɓoye, suna kallon takawata suna a shirye su ɗauki raina.

  20. Duba yadda suka kwanta suna jirana! Mugaye suna ƙulle-ƙullen gāba da ni ba saboda wani dalili ko na yi wa wani zunubi ba, ya Ubangiji.

  21. Ban yi wani laifi ba, duk da haka suna a shirye su fāɗa mini. Tashi ka taimake ni; dubi halin da nake ciki!

  22. Sukan dawo da yamma, suna wage haƙora kamar karnuka, suna yawo a birni.

  23. Dubi abin da suke tofawa daga bakunansu, suna tofar da takuba daga leɓunansu, suna cewa, “Wa zai ji mu?”

  24. Har yaushe za ku tasar wa mutum guda? Dukanku ne za ku kā da shi wannan jinganannen bango, wannan rusasshen katanga?

  25. Sun kintsa sosai su tumɓuke shi daga matsayinsa mai martaba; suna jin daɗi yin ƙarairayi. Sukan sa wa mutum albarka da bakinsu, amma a zuciyarsu la’antawa suke yi. Sela