Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Malice

135 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. wanda yake ƙulla mugunta da ruɗu a cikin zuciyarsa, kullum yana tā-da-na-zaune-tsaye

  2. Saboda haka masifa za tă fāɗa farat ɗaya; za a hallaka shi nan da nan, ba makawa.

  3. Akwai abubuwa shida da Ubangiji ya ƙi, abubuwa bakwai da suke abin ƙyama gare shi,

  4. zuciyar da take ƙulla mugayen dabaru, ƙafafun da suke sauri zuwa aikata mugunta,

  5. mai shaidar ƙarya wanda yake zuba ƙarairayi, da kuma mutumin da yake tā-da-na-zaune-tsaye a cikin ’yan’uwa.

  6. Kada ka yi dariya sa’ad da abokin gāba ya fāɗi; sa’ad da ya yi tuntuɓe, kada ka yi farin ciki,

  7. in ba haka ba in Ubangiji ya gani ba zai amince ba ya kuma juye fushinsa daga gare shi.

  8. Masu zalunci za su ƙare, masu ba’a za su ɓace, kuma dukan waɗanda suke da ido don mugunta za su hallaka,

  9. waɗanda ta magana kawai sukan mai da mutum mai laifi, waɗanda suke kafa tarko wa mai ba da kāriya a ɗakin shari’a da shaidar ƙarya kuma su hana marar laifi samun shari’ar adalci.

  10. Babu wani mai ce a yi adalci; babu wani mai nema a dubi al’amarinsa da mutunci. Sun dogara a gardandamin banza suna ƙarairayi; suna ɗaukar cikin ɓarna, su haifi mugunta.

  11. Suna ƙyanƙyashe ƙwan kāsā su kuma saƙa yanar gizo-gizo. Duk wanda ya ci ƙwansu zai mutu, kuma sa’ad da ƙwan ya fashe, zai ƙyanƙyashe kububuwa.

  12. Yanar gizo-gizonsu ba amfani don tufa; ba za su iya rufuwa da abin da suka yi ba. Ayyukansu mugaye ne, ayyukan tā da hargitsi kuma suna a hannuwansu.

  13. Ƙafafunsu sukan gaggauta zuwa aikata zunubi; suna da saurin zub da jini. Tunaninsu mugaye ne; lalaci da hallaka sun shata hanyoyinsu.

  14. Ko diloli suna ba ’ya’yansu nono su sha, amma mutanena sun zama marasa zuciya kamar jiminai a cikin jeji.

  15. Domin ƙishirwa harshen jarirai ya manne a rufin bakinsu; yaran suna roƙo a ba su burodi, amma ba wanda ya ba su.

  16. Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa domin kun tafa hannuwanku kuka kuma buga ƙafafunku, kuna farin ciki don nuna dukan ƙiyayyarku a kan ƙasar Isra’ila,

  17. saboda haka zan miƙa hannuna gāba da ku in kuma ba da ku ganima ga al’ummai. Zan datse ku daga al’ummai in kuma kore ku daga ƙasashe. Zan hallaka ku, za ku kuwa san cewa ni ne Ubangiji.’ ”

  18. “Ɗan mutum, domin Taya ta yi magana a kan Urushalima ta ce, ‘Yauwa! Ƙofar zuwa al’ummai ta karye, an kuma buɗe mini ƙofofinta; yanzu da take kufai zan wadace,’

  19. saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ina gāba da ke, ya Taya, zan kuwa kawo al’ummai masu yawa su yi gāba da ke, kamar yadda teku takan kawo raƙuman ruwa.

  20. A kan haka, shugabannin nan uku da muƙaddasan nan suka yi ƙoƙari su sami wani laifi a kan Daniyel a yadda yake tafiyar da aikin shugabancinsa, amma ba su samu ba. Ba su same shi da wani laifin cin hanci ba, domin shi amintacce ne kuma babu wani aibi a kansa ko rashin kula.

  21. A ƙarshe waɗannan mutane suka ce; “Ba za mu taɓa samun wani laifin da za mu kama Daniyel da shi ba, sai dai ko abin ya shafi dokar Allahnsa.”

  22. Saboda haka shugabannin nan suka haɗu da muƙaddasan nan suka tafi wurin sarki a ƙungiyance suka ce, “Ya Sarki Dariyus, ranka yă daɗe!

  23. Shugabannin masarauta, da masu mulki, da muƙaddasai, da mashawarta da gwamnoni duk sun amince cewa sarki yă kafa doka yă kuma yi umarni cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda ya yi addu’a ga wani allah ko mutum, in ba a gare ka ba, ya sarki, jefa shi cikin kogon zakoki.

  24. Yanzu, ya sarki, sai ka yi umarni ka kuma yi shi a rubuce saboda kada a canja shi, bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.”

  25. Sai Sarki Dariyus ya ba da umarnin a rubuce.