Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Kwanakina sun fi mai gudu wucewa da sauri; suna firiya babu wani abin jin daɗi a cikinsu.

  2. Suna wucewa kamar jirgin ruwan da aka yi da kyauro, kamar jahurma da ta kai wa namanta cafka.

  3. ‘In na ce zan manta da abin da yake damu na, zan yi murmushi in daina nuna ɓacin rai,’

  4. duk da haka ina tsoron duk wahalata, domin na san ba za ka ɗauke ni marar laifi ba.

  5. Tun da an riga an ɗauke ni mai laifi, duk ƙoƙarina a banza yake.

  6. Ko da na wanke jikina duka da sabulu, na wanke hannuwana kuma da soda,

  7. duk da haka za ka jefa ni cikin ƙazamin wuri, yadda ko rigunan jikina ma za su ƙi ni.

  8. “Shi ba mutum ba ne kamar ni wanda zan iya amsa masa, har da za mu yi faɗa da juna a wurin shari’a.

  9. In da akwai wanda zai iya shiga tsakaninmu, ya ɗora hannunsa a kanmu tare,

  10. wani wanda zai sa Allah yă daina duka na, don yă daina ba ni tsoro.

  11. Sa’an nan ne zan iya yin magana ba tare da jin tsoronsa ba, amma a yadda nake a yanzu ba zan iya ba.

  12. Zan ce wa Allah, kada ka hukunta ni, amma ka gaya mini laifin da na yi maka.

  13. Kana jin daɗin ba ni wahala, don me ka yashe ni, abin da ka halitta da hannunka, yayinda kake murmushi game da shirye-shiryen mugaye?

  14. Idanunka irin na mutum ne? Kana gani yadda mutum yake gani ne?

  15. Kwanakinka kamar na mutane ne, ko shekarunka kamar na mutane ne

  16. da za ka neme ni da laifi ka hukunta ni?

  17. Ko da yake ka san ba ni da laifi, kuma ba wanda zai iya cetona daga hannunka.

  18. “Da hannuwanka ka ƙera ni, kai ka halicce ni. Yanzu kuma kai za ka juya ka hallaka ni?

  19. Ka tuna cewa ka mulmula ni kamar yumɓu. Yanzu za ka mai da ni in zama ƙura kuma?

  20. Ba kai ka zuba ni kamar madara ba, na daskare kamar cuku.

  21. Ka rufe ni da tsoka da fata, ka harhaɗa ni da ƙasusuwa da jijiyoyi?

  22. Ka ba ni rai ka kuma yi mini alheri, kuma cikin tanadinka ka kula da ruhuna.

  23. “Amma wannan shi ne abin da ka ɓoye a zuciyarka, na kuma san abin da yake cikin zuciyarka ke nan.

  24. In na yi zunubi kana kallo na kuma ba za ka fasa ba ni horo ba don laifin da na yi.

  25. Idan ina da laifi, kaitona! Ko da ba ni da laifi, ba zan iya ɗaga fuskata ba, gama kunya ta ishe ni duk ɓacin rai ya ishe ni.