Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai cece ka daga bala’o’i guda shida; har bakwai ma ba abin da zai same ka.

  2. Lokacin yunwa yana tsare ka daga mutuwa, a cikin yaƙi kuma yana kāre ka daga sarar takobi.

  3. “Lalle, na san wannan gaskiya ne. Amma ta yaya mutum zai iya zama mai adalci a gaban Allah?

  4. Ko da mutum yana so yă yi gardama da shi, ba zai taɓa amsa masa ba ko da sau ɗaya cikin dubu.

  5. Hikimarsa tana da zurfi, ikonsa yana da yawa. Wane ne ya taɓa yin faɗa da shi har ya yi nasara?

  6. Yana matsar da manyan duwatsu kafin su sani kuma yana juya su cikin fushinsa.

  7. Yana girgiza ƙasa, yana girgiza harsashenta.

  8. Yana magana da rana sai ta ƙi yin haske; yana hana taurari yin haske.

  9. Shi kaɗai ya shimfiɗa sammai ya kuma yi tafiya a kan raƙuman ruwan teku.

  10. Shi ne ya halicci Mafarauci da Kare da Zomo, da Kaza, da ’Ya’yanta da tarin taurari a sama, da taurarin kudu.

  11. Yana yin abubuwan banmamaki waɗanda ba a iya ganewa, mu’ujizai waɗanda ba a iya ƙirgawa.

  12. Ba na iya ganinsa lokacin da ya wuce ni; ba na sani ya wuce lokacin da ya wuce.

  13. Wane ne ya isa yă hana shi in ya ƙwace abu? Wa zai ce masa, ‘Me kake yi?’

  14. Allah ba ya danne fushinsa; ko dodannin ruwan da ake kira ayarin Rahab ya tattake su.

  15. “Ta yaya zan iya yin faɗa da shi? Ina zan iya samun kalmomin da zan yi gardama da shi?

  16. Ko da yake ba ni da laifi, ba zan iya amsa masa ba; sai dai roƙon jinƙai zan iya yi ga mahukuncina.

  17. Ko da na yi kira gare shi ya amsa mini, ban yarda cewa zai saurare ni ba.

  18. Zai sa hadari yă danne ni yă ƙara mini ciwona ba dalili.

  19. Ba zai bari in yi numfashi ba, sai dai yă ƙara mini azaba.

  20. In maganar ƙarfi ne, shi babban mai ƙarfi ne! In kuma maganar shari’a ne, wa zai kai kararsa?

  21. Ko da ni marar ƙarfi ne, bakina ya isa yă sa in zama mai laifi; in ba ni da laifi, zai sa in yi laifi.

  22. “Ko da yake ba ni da laifi, ban damu da kaina ba; na rena raina.

  23. Ba bambanci; shi ya sa na ce, ‘Yana hallaka marasa laifi da kuma mugaye.’

  24. Lokacin da bala’i ya kawo ga mutuwa, yakan yi dariyar baƙin cikin marasa laifi.

  25. Lokacin da ƙasa ta faɗa a hannun mugaye, yakan rufe idanun masu shari’a. In ba shi ba wa zai yi wannan?