Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da God

662 ayoyi · 46 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji kuwa ya furta a wannan rana cewa ku mutanensa ne, mallakarsa kamar yadda ya yi alkawari, da kuma cewa za ku kiyaye dukan umarnansa.

  2. Ya furta cewa zai sa ku zama masu yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al’umman da ya yi. Za ku zama jama’a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku, kamar yadda ya yi alkawari.

  3. Ubangiji zai kafa ku kamar mutanensa masu tsarki, kamar yadda ya yi alkawari da rantsuwa, in kun kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi tafiya a hanyoyinsa.

  4. Sa’an nan dukan mutane a duniya za su ga cewa ana kiranku da sunan Ubangiji, za su kuwa ji tsoronku.

  5. Gama rabon Ubangiji shi ne mutanensa, Yaƙub shi ne rabon gādonsa.

  6. A cikin hamada ya same shi, a jeji marar amfani, inda namomi suke kuka. Ya tsare shi, ya kuma lura da shi; ya bi da shi kamar ƙwayar idonsa,

  7. kamar gaggafar da take yawo a kan sheƙarta tana rufe ’ya’yanta, ta buɗe fikafikanta don tă kwashe su tă ɗauke su a kafaɗunta.

  8. Ubangiji kaɗai ya jagorance shi; babu wani baƙon gunkin da yake tare da shi.

  9. Zan zama Ubansa, shi kuma yă zama ɗana. Idan ya yi laifi, zan yi amfani da mutane in hukunta shi. Mutane ne za su zama bulalata.

  10. Amma ba za a taɓa ɗauke ƙaunata daga gare shi yadda na ɗauke ta daga wurin Shawulu ba, shi wannan wanda na kawar daga gabanka.

  11. Wane ne kuma yake kamar da mutanenka Isra’ila, al’umma guda a duniya wadda Allah ya fita don yă kuɓutar wa kansa, ya kuma yi suna wa kansa, ya kuma aikata manyan abubuwa da kuma al’amuran banmamaki ta wurin korin al’ummai da allolinsu daga gaban mutanenka, waɗanda ka kuɓutar daga Masar?

  12. Ka kafa mutanenka Isra’ila kamar naka na kanka har abada, kai kuma, ya Ubangiji, ka zama Allahnsu.

  13. ya ce, “Ya Ubangiji, Allah na Isra’ila, babu Allah kamar ka a sama can bisa, ko a ƙasa can ƙarƙashi, kai da kake kiyaye alkawarinka na ƙauna ga bayinka waɗanda suke cin gaba a hanyarka da dukan zuciyarsu.

  14. Ka kiyaye alkawarinka da ka yi wa bawanka Dawuda mahaifina. Da bakinka ka yi alkawari, da hannunka kuma ka cika shi, yadda yake a yau.

  15. Gama su mutanenka ne, abin gādonka, waɗanda ka fitar daga Masar, daga tanderu mai narken ƙarfe.

  16. “Bari idanunka su buɗe ga roƙon bawanka, ga roƙon mutanenka Isra’ila, bari kuma ka saurare su sa’ad da suka yi kuka gare ka.

  17. Gama ka ware su daga dukan al’umman duniya su zama abin gādonka, kamar yadda aka furta ta wurin bawanka Musa sa’ad da kai, ya Ubangiji Mai Iko Duka ka fitar da kakanninmu daga Masar.”

  18. Sa’an nan ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda da hannuwansa ya cika abin da ya yi alkawari da bakinsa ga mahaifina Dawuda. Gama ya ce,

  19. ‘Tun ranar na da fitar da mutanena daga Masar, ban zaɓi wani birni a wata kabilar Isra’ila don a gina haikali domin Sunana ya kasance a can ba, ba kuwa zaɓi wani yă zama shugaba a bisa jama’ata Isra’ila ba.

  20. Amma yanzu na zaɓi Urushalima domin Sunana yă kasance a can, na kuma zaɓi Dawuda yă yi mulkin mutanena Isra’ila.’

  21. “Mahaifina Dawuda ya yi niyya a zuciyarsa yă gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  22. Amma Ubangiji ya ce wa mahaifina Dawuda, ‘Domin yana a zuciyarka ka gina haikali domin Sunana, ka yi daidai da ka kasance da wannan a zuciyarka.

  23. Duk da haka, ba kai ba ne za ka gina haikalin, amma ɗanka wanda yake namanka da jininka, shi ne wanda zai gina haikali domin Sunana.’

  24. “Ubangiji ya kiyaye alkawarin da ya yi. Na gāje Dawuda mahaifina yanzu kuwa na zauna a kan kujerar sarautar Isra’ila, kamar dai yadda Ubangiji ya alkawarta, na kuma gina haikali domin Sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila.

  25. A can na ajiye akwatin alkawari, inda alkawarin Ubangiji da ya yi da mutanen Isra’ila yake.”