Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abraham

314 ayoyi · 39 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.

  2. Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”

  3. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.

  4. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.

  5. Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske.

  6. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku.

  7. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”

  8. Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi.

  9. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba.

  10. Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.

  11. Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”

  12. Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.

  13. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa.

  14. Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”

  15. Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”

  16. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!”

  17. Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.

  18. Game da wannan ya amsa ya ce, “’Yan’uwa da ubanni, ku saurare ni! Allah mai ɗaukaka ya bayyana ga kakanmu Ibrahim yayinda yake a ƙasar Mesofotamiya tukuna, kafin ya yi zama a Haran.

  19. Allah ya ce, ‘Ka bar ƙasarka da kuma mutanenka, ka tafi ƙasar da zan nuna maka.’

  20. “Saboda haka ya bar ƙasar Kaldiyawa ya kuma yi zama a Haran. Bayan mutuwar mahaifinsa, Allah ya aika da shi wannan ƙasar da yanzu kuke zama.

  21. To, me za mu ce Ibrahim kakan kakanninmu ya gani game da wannan batu?

  22. In fa da gaske ne Ibrahim ya sami kuɓuta ta wurin ayyuka, yana da abin da zai yin taƙama da shi ke nan, amma ba a gaban Allah ba.

  23. Me Nassin ya ce? “Ibrahim ya gaskata Allah, aka kuma lissafta wannan adalci ne a gare shi.”

  24. To, sa’ad da mutum ya yi aiki, ba a lissafta ladan aikinsa a matsayin kyauta, sai dai a matsayin hakkinsa.

  25. Amma fa, game da mutumin da ba ya aiki sai dai dogara ga Allah wanda yake kuɓutar da masu mugunta, akan lissafta bangaskiyarsa a matsayin adalci ne.