Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abraham: In Paradise

12 ayoyi · 39 fannoni

Ayoyi game da In Paradise

  1. Ina kuma gaya muku da yawa za su zo daga gabas da kuma yamma, su ɗauki wuraren zamansu a biki tare da Ibrahim, Ishaku, da Yaƙub a cikin mulkin sama.

  2. “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.

  3. “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.

  4. A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.

  5. Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

  6. “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.

  7. Ban da wannan duka ma, tsakaninmu da kai, akwai wani babban rami da aka yi, yadda waɗanda suke son ƙetarewa daga nan zuwa wurinku, ba za su iya ba, kuma ba mai iya ƙetarewa daga wurinku zuwa wurinmu.’

  8. “Ya amsa ya ce, ‘To, ina roƙonka, ya uba, ka aiki Lazarus zuwa gidan mahaifina,

  9. gama ina da ’yan’uwana biyar maza. Bari yă ba su gargaɗi, don kada su ma su zo wurin nan mai azaba.’

  10. “Ibrahim ya amsa ya ce, ‘Suna da Musa da Annabawa, ai, sai su saurare su.’

  11. “Sai ya ce, ‘A’a, ya uba, Ibrahim, in dai wani ya tashi daga matattu ya je wurinsu, za su tuba.’

  12. “Amma ya ce masa, ‘In ba su saurari Musa da Annabawa ba, kai, ko da wani ya tashi daga matattu ma, ba za su saurare shi ba.’ ”