Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abraham: Children of

10 ayoyi · 39 fannoni

Ayoyi game da Children of

  1. Haka fa Hagar ta haifa wa Abram ɗa, Abram kuwa ya ba da suna Ishmayel ga ɗan da ta haifa.

  2. Saratu ta yi ciki, ta kuma haifa wa Ibrahim ɗa a tsufansa; a daidai lokacin da Allah ya yi masa alkawari.

  3. Ibrahim ya sa wa ɗan da Saratu ta haifa masa suna Ishaku.

  4. Ibrahim ya auro wata mace, mai suna Ketura.

  5. Ta haifa masa Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa.

  6. Yokshan shi ne mahaifin Sheba da Dedan. Zuriyar Dedan su ne mutanen Ashur, da mutanen Letush, da kuma mutanen Lewummin.

  7. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida, da kuma Elda’a. Dukan waɗannan zuriyar Ketura ce.

  8. ’Ya’yan Ketura maza, ƙwarƙwarar Ibrahim su ne, Zimran, Yokshan, Medan, Midiyan, Ishbak da Shuwa. ’Ya’yan Yokshan maza su ne, Sheba da Dedan.

  9. ’Ya’yan Midiyan maza su ne, Efa, Efer, Hanok, Abida da Elda’a. Dukan waɗannan su ne zuriyar Ketura.

  10. Ibrahim shi ne mahaifin Ishaku. ’Ya’yan Ishaku maza su ne, Isuwa da Isra’ila.