Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Abraham: How regarded by his descendants

20 ayoyi · 39 fannoni

Ayoyi game da How regarded by his descendants

  1. Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.

  2. Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”

  3. “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje.

  4. Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.

  5. Sai suka amsa masa suka ce, “Ai, mu zuriyar Ibrahim ne kuma ba mu taɓa bauta wa kowa ba. Yaya za ka ce za a ’yantar da mu?”

  6. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.

  7. Bawa dai ba shi da wurin zama na ɗinɗinɗin a cikin iyali, amma ɗa na gida ne har abada.

  8. Saboda haka in Ɗan ya ’yantar da ku, za ku ’yantu da gaske.

  9. Na dai san ku zuriyar Ibrahim ne. Duk da haka kuna shiri ku kashe ni, don maganata ba ta da wurin zama a cikinku.

  10. Ina faɗi muku abin da na gani a wurin Ubana, ku kuwa kuna yin abin da kuka ji daga wurin ubanku.”

  11. Suka ce, “To, ai, Ibrahim ne mahaifinmu.” Yesu ya ce, “Da ku ’ya’yan Ibrahim ne, da za ku aikata abubuwan da Ibrahim ya yi.

  12. Ga shi kun ƙudura, sai kun kashe ni, ni mutumin da ya faɗa muku gaskiyar da na ji daga Allah. Ibrahim bai yi irin waɗannan abubuwa ba.

  13. Da jin haka Yahudawa suka ce, “Tabɗi, yanzu kam mun san kana da aljani! Ibrahim ya mutu haka ma annabawa, ga shi kana cewa duk wanda ya kiyaye maganarka ba zai ɗanɗana mutuwa ba sam.

  14. Ka fi Ibrahim mahaifinmu ne? Ya mutu, haka ma annabawa. Wa kake ɗauka kanka ne?”

  15. Yesu ya amsa ya ce, “In ma na ɗaukaka kaina, ɗaukakata ba kome ba ce. Ubana, wanda kuke cewa shi ne Allahnku, shi ne wanda yake ɗaukaka ni.

  16. Ko da yake ba ku san shi ba, ni dai na san shi. In kuwa na ce ban san shi ba, na zama maƙaryaci kamar ku ke nan, amma na san shi, kuma ina kiyaye maganarsa.

  17. Mahaifinku Ibrahim ya yi farin ciki sosai yă sami ganin ranata; ya kuwa gan ta, ya yi murna.”

  18. Sai Yahudawa suka ce masa, “Kai, shekarunka har yanzu ba su kai hamsin tukuna ba fa, har ka ga Ibrahim!”

  19. Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake gaya muku, tun ba a haifi Ibrahim ba, ni ne!”

  20. Da jin haka sai suka ɗebo duwatsu don su jajjefe shi, amma Yesu ya ɓuya, ya fita daga filin haikali.