Tsallake zuwa abun ciki

circa 970–930 BC

Solomon & The Temple

Solomon builds the great Temple in Jerusalem and rules with unprecedented wisdom and wealth before foreign gods divide his heart.

635 ayoyi · 2 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. 1 Sarakuna 8:58kusan 1004 K.H.

    Bari yă juye zukatanmu gare shi, don mu yi tafiya a cikin dukan hanyoyinsa, mu kuma kiyaye umarnansa, ƙa’idodinsa, da kuma farillan da ya ba wa kakanninmu.

  2. 1 Sarakuna 8:59kusan 1004 K.H.

    Bari kuma waɗannan kalmomina, waɗanda na yi addu’a a gaban Ubangiji, su yi kusa da Ubangiji Allahnmu, dare da rana, don yă biya bukatan bawansa da na mutanensa Isra’ila, bisa ga bukatan kowa,

  3. 1 Sarakuna 8:60kusan 1004 K.H.

    saboda dukan mutanen duniya su san cewa Ubangiji, shi ne Allah, babu kuma wani.

  4. 1 Sarakuna 8:61kusan 1004 K.H.

    Amma dole ku miƙa zukatanku ga Ubangiji Allahnmu, don ku rayu, ta wurin bin ƙa’idodinsa, ku kuma yi biyayya da umarnansa, kamar yadda kuke yi a wannan lokaci.”

  5. 1 Sarakuna 8:62kusan 1004 K.H.

    Sai sarki da dukan Isra’ila, suka miƙa hadayu a gaban Ubangiji.

  6. 1 Sarakuna 8:63kusan 1004 K.H.

    Solomon ya miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, shanu dubu ashirin da biyu, tumaki da awaki dubu ɗari da dubu ashirin. Ta haka sarki da dukan Isra’ilawa suka keɓe haikalin Ubangiji.

  7. 1 Sarakuna 8:64kusan 1004 K.H.

    A wannan rana sarki ya tsarkake sashe na tsakiyar fili a gaban haikalin Ubangiji, a can kuma ya miƙa hadaya ta ƙonawa, hadaya ta gari, da kitsen hadaya ta salama, gama bagaden tagulla a gaban Ubangiji ya yi ƙanƙanta sosai da za a miƙa hadayun ƙonawa, hadayun hatsi, da kuma kitsen hadayun salama.

  8. 1 Sarakuna 8:65kusan 1004 K.H.

    Ta haka Solomon da dukan Isra’ila, wato, babban taro, suka yi bikin a lokacin. Mutane suka zo, tun daga Lebo Hamat har zuwa Rafin Masar. Suka yi biki a gaban Ubangiji Allahnmu, kwana bakwai. Suka kuma ƙara kwana bakwai, kwanaki goma sha huɗu gaba ɗaya.

  9. 1 Sarakuna 8:66kusan 1004 K.H.

    A rana ta biye sai ya sallame mutane. Suka sa wa sarki albarka, sa’an nan suka watse zuwa gida, da farin ciki, da murna a zukatansu saboda kyawawan abubuwan da Ubangiji ya yi domin bawansa Dawuda, da kuma mutanensa Isra’ila.

  10. 1 Sarakuna 9:1kusan 991 K.H.

    Sa’ad da Solomon ya gama ginin haikalin Ubangiji da kuma fadan sarki, ya kuma yi dukan abin da yake so yă yi,

  11. 1 Sarakuna 9:2kusan 991 K.H.

    sai Ubangiji ya bayyana gare shi sau na biyu, kamar yadda ya bayyana masa a Gibeyon.

  12. 1 Sarakuna 9:3kusan 991 K.H.

    Ubangiji ya ce masa, “Na ji addu’arka da kuma roƙon da ka yi a gabana; na tsarkake wannan haikali wanda ka gina, ta wurinsa Sunana zai kasance a can har abada. Idanuna da zuciyata kullum za su kasance a can.

  13. 1 Sarakuna 9:4kusan 991 K.H.

    “Kai kuwa, in ka yi tafiya a gabana da mutunci a zuci da kuma gaskiya, kamar yadda Dawuda mahaifinka ya yi, ka yi dukan abin da na umarta, ka kuma yi biyayya da ƙa’idodina da kuma dokokina,

  14. 1 Sarakuna 9:5kusan 991 K.H.

    zan kafa kujerar sarautarka a bisa Isra’ila har abada, kamar yadda na alkawarta wa Dawuda mahaifinka sa’ad da na ce, ‘Ba za ka taɓa rasa wani a kan kujerar sarautar Isra’ila ba.’

  15. 1 Sarakuna 9:6kusan 991 K.H.

    “Amma in kai, ko ’ya’yanka maza, suka juye daga gare ni, ba ku kuma kiyaye umarnai da ƙa’idodin da na ba ku ba, kuka yi gaba, kuka bauta wa waɗansu alloli, kuka kuma yi musu sujada,

  16. 1 Sarakuna 9:7kusan 991 K.H.

    sai in yanke mutanen Isra’ila daga ƙasar da na ba su, in kuma ƙi wannan haikalin da na tsarkake domin Sunana. Isra’ila kuwa za tă zama abin gori da abin dariya a cikin dukan mutane.

  17. 1 Sarakuna 9:8kusan 991 K.H.

    Wannan haikali zai zama tarin juji. Duk wanda ya wuce ta hanyan nan kuwa zai ji tausayi, yă kuma yi tsaki yana cewa, ‘Me ya sa Ubangiji ya yi haka ga wannan ƙasa da kuma wannan haikali?’

  18. 1 Sarakuna 9:9kusan 991 K.H.

    Mutane za su amsa su ce, ‘Saboda sun yashe Ubangiji Allahnsu, wanda ya fitar da su daga Masar, suka rungumi waɗansu alloli, suna yin musu sujada, suna bauta musu ne, ya sa Ubangiji ya kawo dukan masifan nan a kansu.’ ”

  19. 1 Sarakuna 9:10kusan 991 K.H.

    A ƙarshen shekaru ashirin da Solomon ya ɗauka yana gina haikalin Ubangiji da fadan sarki,

  20. 1 Sarakuna 9:11kusan 991 K.H.

    sai Sarki Solomon ya ba wa Hiram sarkin Taya garuruwa ashirin a yankin Galili, gama Hiram ya tanada masa da dukan katakai al’ul da na fir, da kuma zinariyar da ya bukaci domin aiki.

  21. 1 Sarakuna 9:12kusan 991 K.H.

    Amma sa’ad da Hiram ya zo daga Taya don yă ga garuruwan da Solomon ya ba shi, sai bai ji daɗi ba.

  22. 1 Sarakuna 9:13kusan 991 K.H.

    Sai ya ce, “Wanda irin garuruwa ke nan ka ba ni, ɗan’uwana?” Saboda haka ya kira su Ƙasar Kabul, sunan da suke da shi har wa yau.

  23. 1 Sarakuna 9:14kusan 991 K.H.

    Hiram kuwa ya aika wa sarki talenti 120 na zinariya.

  24. 1 Sarakuna 9:15kusan 1015 K.H.

    Ga lissafin ma’aikatan gandun da Sarki Solomon ya ɗauka don ginin haikalin Ubangiji, da fadarsa, da madogaran gini, da katangar Urushalima, da kuma Hazor Megiddo da Gezer.

  25. 1 Sarakuna 9:16kusan 1015 K.H.

    (Fir’auna sarkin Masar ya kai wa Gezer hari, ya kuma ci ta da yaƙi. Ya sa mata wuta, ya kashe Kan’aniyawanta mazaunan wurin, ya kuma ba da ita a matsayin kyautar aure ga ’yarsa, matar Solomon.