Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Filibbiyawa 1:20kusan 64 M.

    Ina saurara da marmari da kuma bege cewa ba zan taɓa shan kunya ba, sai dai zan sami issashen ƙarfin hali yanzu kamar kullum, za a ɗaukaka Kiristi a jikina, ko ta wurin rayuwa ko kuma ta wurin mutuwa.

  2. Filibbiyawa 1:21kusan 64 M.

    Gama a gare ni, rai Kiristi ne, mutuwa kuma riba ce.

  3. Filibbiyawa 1:22kusan 64 M.

    In zan ci gaba da rayuwa a cikin jiki, wannan zai zama aiki mai amfani a gare ni. Duk da haka me zan zaɓa? Ban sani ba!

  4. Filibbiyawa 1:23kusan 64 M.

    Na rasa wanda zan zaɓa cikin biyun nan. Ina sha’awa in yi ƙaura in zauna tare da Kiristi, wannan kuwa ya fi kyau nesa ba kusa ba;

  5. Filibbiyawa 1:24kusan 64 M.

    amma ya fi muku muhimmanci in rayu cikin jiki.

  6. Filibbiyawa 1:25kusan 64 M.

    Na tabbata haka ne, na kuwa san zan wanzu in zauna tare da ku duka, domin ku ci gaba, bangaskiyarku tana sa ku farin ciki,

  7. Filibbiyawa 1:26kusan 64 M.

    domin ta wurin kasancewata tare da ku, farin cikinku cikin Kiristi Yesu zai cika sosai ta dalilina.

  8. Filibbiyawa 1:27kusan 64 M.

    Kome ya faru, ku yi zaman da ya cancanci bisharar Kiristi. Ta haka, ko na zo na gan ku, ko ban zo ba, in ji labari cewa kun tsaya da ƙarfi a cikin ruhu ɗaya, kuna fama kamar mutum ɗaya saboda bangaskiyar bishara

  9. Filibbiyawa 1:28kusan 64 M.

    ba tare da kun ji tsoron waɗanda suke gāba da ku ta kowace hanya ba. Wannan alama ce a gare su cewa za a hallaka su, amma a gare ku za a cece ku, wannan tabbacin kuwa daga wurin Allah ne.

  10. Filibbiyawa 1:29kusan 64 M.

    Gama an ba ku zarafi a madadin Kiristi cewa ba gaskatawa da shi kaɗai ba kuka yi ba, har ma ku sha wahala dominsa,

  11. Filibbiyawa 1:30kusan 64 M.

    da yake kuna shan faman da kuka gan na sha, kuna kuma jin cewa har yanzu ina sha.

  12. Filibbiyawa 2:1kusan 64 M.

    In kuna da wata ƙarfafawa daga tarayya da Kiristi, in da wata ta’aziyya daga ƙaunarsa, in da wani zumunci da Ruhu, in da juyayi da tausayi,

  13. Filibbiyawa 2:2kusan 64 M.

    to, sai ku sa farin cikina yă zama cikakke ta wurin kasance da hali ɗaya, kuna ƙauna ɗaya, kuna zama ɗaya cikin ruhu da kuma manufa.

  14. Filibbiyawa 2:3kusan 64 M.

    Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.

  15. Filibbiyawa 2:4kusan 64 M.

    Bai kamata kowannenku yă kula da sha’anin kansa kawai ba, sai dai yă kula da sha’anin waɗansu ma.

  16. Filibbiyawa 2:5kusan 64 M.

    A cikin dangantakarku da juna, ya kamata halayenku su zama kamar na Kiristi Yesu.

  17. Filibbiyawa 2:6kusan 64 M.

    Wanda, ko da yake cikin ainihin surar Allah yake, bai mai da daidaitakansa nan da Allah wani abin riƙewa kam-kam ba,

  18. Filibbiyawa 2:7kusan 64 M.

    amma ya mai da kansa ba kome ba, yana ɗaukan ainihin surar bawa, aka yi shi cikin siffar mutum.

  19. Filibbiyawa 2:8kusan 64 M.

    Aka kuma same shi a kamannin mutum, ya ƙasƙantar da kansa ya kuma zama mai biyayya wadda ta kai shi har mutuwa, mutuwar ma ta gicciye!

  20. Filibbiyawa 2:9kusan 64 M.

    Saboda haka Allah ya ɗaukaka shi zuwa mafificin wuri ya kuma ba shi sunan da ya fi dukan sunaye,

  21. Filibbiyawa 2:10kusan 64 M.

    don a sunan Yesu kowace gwiwa za tă durƙusa, a sama da a ƙasa da kuma a ƙarƙashin ƙasa,

  22. Filibbiyawa 2:11kusan 64 M.

    kowane harshe kuma yă furta cewa Yesu Kiristi Ubangiji ne, don ɗaukakar Allah Uba.

  23. Filibbiyawa 2:12kusan 64 M.

    Saboda haka, ya abokaina ƙaunatattu, kamar yadda kullum kuke biyayya ba kawai sa’ad da ina nan ba, amma yanzu da ba na nan tare da ku, ku ci gaba da yin ayyukan cetonku da tsoro da kuma rawan jiki,

  24. Filibbiyawa 2:13kusan 64 M.

    gama Allah ne yake aiki a cikinku, don ku nufa ku kuma aikata bisa ga nufinsa mai kyau.

  25. Filibbiyawa 2:14kusan 64 M.

    Ku yi kome ba tare da gunaguni ko gardama ba,