Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Filibbiyawa 3:10kusan 64 M.

    Ina so in san Kiristi da ikon tashinsa daga matattu da kuma zumuncin tarayya cikin shan wahalarsa, in kuma zama kamar sa a cikin mutuwarsa,

  2. Filibbiyawa 3:11kusan 64 M.

    yadda kuma ko ta yaya, in kai ga tashin nan daga matattu.

  3. Filibbiyawa 3:12kusan 64 M.

    Ba cewa na riga na sami dukan wannan ba ne, ko kuma an riga an mai da ni cikakke ba, sai dai ina nacewa don in kai ga samun abin da Kiristi Yesu ya riƙe ni saboda shi.

  4. Filibbiyawa 3:13kusan 64 M.

    ’Yan’uwa, ban ɗauki kaina a kan cewa na riga na sami abin ba. Sai dai abu guda nake yi. Ina mantawa da abin da yake baya, ina kuma nacewa zuwa ga samun abin da yake gaba,

  5. Filibbiyawa 3:14kusan 64 M.

    ina nacewa gaba zuwa ga manufar, don in sami ladar da Allah ya yi mini na kiran nan zuwa sama a cikin Kiristi Yesu.

  6. Filibbiyawa 3:15kusan 64 M.

    Dukanmu da muka balaga ya kamata mu yi wannan irin ganin abubuwa. In kuwa saboda wani dalili tunaninku ya yi dabam, Allah zai bayyana muku wannan ma.

  7. Filibbiyawa 3:16kusan 64 M.

    Sai dai a duk inda muka kai, mu ci gaba da haka.

  8. Filibbiyawa 3:17kusan 64 M.

    Ku haɗa kai da waɗansu cikin bin gurbina, ku kuma lura da waɗanda suke rayuwa bisa ga ƙa’idar da muka ba ku.

  9. Filibbiyawa 3:18kusan 64 M.

    Gama kamar yadda na sha gaya muku yanzu kuma ina sāke gaya muku har ma da hawaye, waɗansu da yawa suna rayuwa kamar abokan gāban gicciyen Kiristi.

  10. Filibbiyawa 3:19kusan 64 M.

    Ƙaddararsu hallaka ce, allahnsu cikinsu ne, rashin kunyarsu shi ne abin fahariyarsu. Hankalinsu yana kan kayan duniya.

  11. Filibbiyawa 3:20kusan 64 M.

    Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi,

  12. Filibbiyawa 3:21kusan 64 M.

    shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.

  13. Filibbiyawa 4:1kusan 64 M.

    Saboda haka ’yan’uwana, ku da nake ƙauna, nake kuma marmarin ganinku, ku da kuke farin cikina da kuma rawanina, ku dāge ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna!

  14. Filibbiyawa 4:2kusan 64 M.

    Ina roƙon Yuwodiya ina kuma roƙon Sintike, su yi zaman lafiya da juna saboda su na Ubangiji ne.

  15. Filibbiyawa 4:3kusan 64 M.

    I, ina kuma roƙonka, abokin famata, ka taimaki matan nan waɗanda suka yi fama aikin bishara tare da ni, haka ma Kilemen da kuma sauran abokan aikina, waɗanda sunayensu suna cikin littafin rai.

  16. Filibbiyawa 4:4kusan 64 M.

    Ku yi farin ciki a cikin Ubangiji kullum. Ina sāke gaya muku ku yi farin ciki!

  17. Filibbiyawa 4:5kusan 64 M.

    Bari kowa yă kasance da sauƙinkai. Ubangiji ya yi kusan zuwa.

  18. Filibbiyawa 4:6kusan 64 M.

    Kada ku damu game da kome sai dai a cikin abu duka, ku gabatar da roƙe-roƙenku ga Allah ta wurin addu’a da roƙo, tare da godiya.

  19. Filibbiyawa 4:7kusan 64 M.

    Salamar Allah, wadda ta wuce dukan fahimta, za tă tsai da zukatanku da tunaninku cikin Kiristi Yesu.

  20. Filibbiyawa 4:8kusan 64 M.

    A ƙarshe, ’yan’uwa, duk abin da yake na gaskiya, duk abin da yake na girmamawa, duk abin da yake daidai, duk abin da yake da tsarki, duk abin da yake kyakkyawa, duk abin da yake na sha’awa, in ma wani abu mafifici ne, ko ya cancanci yabo, ku yi tunani a kan irin abubuwan nan.

  21. Filibbiyawa 4:9kusan 64 M.

    Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

  22. Filibbiyawa 4:10kusan 64 M.

    Na yi farin ciki sosai ga Ubangiji don yanzu kun sāke nuna kun kula da ni. Ko da yake dā ma kun kula da ni sai dai ba ku sami dama ku nuna mini ba.

  23. Filibbiyawa 4:11kusan 64 M.

    Ba na faɗin haka domin ina cikin bukata, gama na koya yadda zan gamsu a cikin kowane hali.

  24. Filibbiyawa 4:12kusan 64 M.

    Na san mene ne zaman rashi, na kuma san mene ne zaman samu. Zan iya zama cikin kowane hali, ko cikin ƙoshi ko cikin yunwa, ko cikin yalwa ko kuma cikin fatara.

  25. Filibbiyawa 4:13kusan 64 M.

    Ina iya yin kome ta wurin wannan wanda yake ba ni ƙarfi.