Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Filibbiyawa 2:15kusan 64 M.

    don ku zama marasa abin zargi, sahihai ’ya’yan Allah, waɗanda ba su da laifi, a zamanin mutane karkatattu, kangararru, waɗanda kuke haskakawa a cikinsu kamar fitilu a duniya

  2. Filibbiyawa 2:16kusan 64 M.

    kuna kuwa cin gaba da riƙe maganar rai domin in yi taƙama a ranar Kiristi cewa ban yi gudu ko fama a banza ba.

  3. Filibbiyawa 2:17kusan 64 M.

    Amma ko da ana tsiyaye jinina kamar hadaya ta sha a kan hadaya da kuma hidimar da take fitowa daga bangaskiyarku, ina murna ina kuma farin ciki da ku duka.

  4. Filibbiyawa 2:18kusan 64 M.

    Haka ma ya kamata ku yi murna ku kuma yi farin ciki tare da ni.

  5. Filibbiyawa 2:19kusan 64 M.

    Ina sa rai a cikin Ubangiji Yesu cewa zan aika da Timoti zuwa gare ku ba da daɗewa ba, don ni ma in ji daɗi sa’ad da na ji labarinku.

  6. Filibbiyawa 2:20kusan 64 M.

    Ba ni da wani kamar sa, wanda yake da ainihin sha’awa a zaman lafiyarku.

  7. Filibbiyawa 2:21kusan 64 M.

    Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.

  8. Filibbiyawa 2:22kusan 64 M.

    Amma, ai, kun san darajar Timoti yadda muka yi bautar bishara tare, kamar ɗa da mahaifinsa.

  9. Filibbiyawa 2:23kusan 64 M.

    Saboda haka, ina sa rai, in aike shi da zarar na ga yadda abubuwa suke a nan.

  10. Filibbiyawa 2:24kusan 64 M.

    Ni kuma ina da tabbaci a cikin Ubangiji cewa zan zo ba da daɗewa ba.

  11. Filibbiyawa 2:25kusan 64 M.

    Amma ina gani ya dace in aika da Afaforiditus, ɗan’uwana, abokin aikina da kuma abokin famana, wanda kuma yake ɗan saƙonku, wanda kuka aika domin yă biya mini bukatuna.

  12. Filibbiyawa 2:26kusan 64 M.

    Gama yana marmarin ganinku duka ya kuma damu domin kun ji cewa ya yi rashin lafiya.

  13. Filibbiyawa 2:27kusan 64 M.

    Ba shakka ya yi rashin lafiya, har ya kusa mutuwa. Amma Allah ya nuna masa jinƙai, ba shi kaɗai ba amma har da ni ma, don yă rage mini baƙin ciki kan baƙin ciki.

  14. Filibbiyawa 2:28kusan 64 M.

    Saboda haka na yi niyya ƙwarai in aike shi wurinku, don sa’ad da kuka sāke ganinsa za ku yi murna, ni kuma in rage damuwa.

  15. Filibbiyawa 2:29kusan 64 M.

    Ku marabce shi cikin Ubangiji da farin ciki mai yawa, ku kuma girmama mutane irinsa,

  16. Filibbiyawa 2:30kusan 64 M.

    domin ya kusa yă mutu saboda aikin Kiristi, ya yi kasai da ransa don yă cikasa taimakon da ba ku iya yi mini ba.

  17. Filibbiyawa 3:1kusan 64 M.

    A ƙarshe, ’yan’uwana, ku yi farin ciki a cikin Ubangiji! Ba abin damuwa ba ne a gare ni in sāke rubuta muku irin waɗannan abubuwa, domin lafiyarku ne.

  18. Filibbiyawa 3:2kusan 64 M.

    Ku yi hankali da waɗancan karnuka, waɗancan mutane masu aikata mugunta, waɗancan masu yankan jiki.

  19. Filibbiyawa 3:3kusan 64 M.

    Gama mu ne masu kaciya, mu da muke yi sujada ta wurin Ruhun Allah, mu da muke taƙama a cikin Kiristi Yesu, mu da ba mu dogara da ayyukan da ake gani ba,

  20. Filibbiyawa 3:4kusan 64 M.

    ko da yake ni kaina ina da dalilan dogara da haka. In kuwa akwai wani wanda yake tsammani yana da dalilan dogara ga jiki, ni fa na fi shi,

  21. Filibbiyawa 3:5kusan 64 M.

    an yi mini kaciya a rana ta takwas, asalina Isra’ila ne, na kabilar Benyamin, mutumin Ibraniyawa ɗan Ibraniyawa; bisa ga doka kuwa ni Bafarisiye ne;

  22. Filibbiyawa 3:6kusan 64 M.

    wajen himma kuwa, ni mai tsananta wa ikkilisiya ne, wajen aikin adalci bisa ga hanyar doka, ni marar laifi ne.

  23. Filibbiyawa 3:7kusan 64 M.

    Amma abin da dā ya zama mini riba yanzu, na ɗauka hasara ce saboda Kiristi.

  24. Filibbiyawa 3:8kusan 64 M.

    Me kuma ya fi, na ɗauki dukan abubuwa hasara ne in aka kwatanta da mafificiyar girman sanin Kiristi Yesu Ubangijina, wanda saboda shi ne na yi hasarar kome. Na mai da su kayan wofi, domin in sami Kiristi

  25. Filibbiyawa 3:9kusan 64 M.

    a kuma same ni a cikinsa, ba da wani adalcin kaina wanda yake zuwa daga bin doka ba, sai dai adalcin da yake samuwa ta wurin bangaskiya a cikin Kiristi, adalcin da yake fitowa daga Allah da kuma yake zuwa ta wurin bangaskiya.