circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Afisawa 6:19kusan 64 M.
Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara,
- Afisawa 6:20kusan 64 M.
wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
- Afisawa 6:21kusan 64 M.
Tikikus, ƙaunataccen ɗan’uwa da kuma amintaccen bawa cikin Ubangiji, zai faɗa muku kome, domin ku ma ku san yadda nake, da kuma abin da nake yi.
- Afisawa 6:22kusan 64 M.
Na aike shi gare ku musamman don wannan, domin ku san yadda muke, yă kuma ƙarfafa ku.
- Afisawa 6:23kusan 64 M.
’Yan’uwa, salama tare da ƙauna da kuma bangaskiya daga Allah Uba da Ubangiji Yesu Kiristi su kasance tare da ku.
- Afisawa 6:24kusan 64 M.
Alheri yă tabbata ga dukan masu ƙaunar Ubangiji Yesu Kiristi da ƙauna marar ƙarewa.
- Filibbiyawa 1:1kusan 64 M.
Bulus da Timoti, bayin Kiristi Yesu, Zuwa ga dukan tsarkaka cikin Kiristi Yesu a Filibbi, tare da masu kula da Ikkilisiya da kuma masu hidima.
- Filibbiyawa 1:2kusan 64 M.
Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare ku.
- Filibbiyawa 1:3kusan 64 M.
Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.
- Filibbiyawa 1:4kusan 64 M.
A cikin dukan addu’o’ina dominku duka, nakan yi addu’a da farin ciki kullum
- Filibbiyawa 1:5kusan 64 M.
saboda tarayyarku a cikin bishara daga ranar farko har yă zuwa yanzu,
- Filibbiyawa 1:6kusan 64 M.
da tabbacin cewa wanda ya fara kyakkyawan aikin nan a cikinku, zai kai shi ga kammalawa har yă zuwa ranar Kiristi Yesu.
- Filibbiyawa 1:7kusan 64 M.
Daidai ne in yi wannan tunani game da dukanku, da yake kuna a zuciyata; domin ko ina daure cikin sarƙoƙi ko ina kāre bishara ina kuma tabbatar da ita, dukanku kuna tarayya cikin alherin Allah tare da ni.
- Filibbiyawa 1:8kusan 64 M.
Allah shi ne shaidata, ya san yadda nake ƙaunarku duka da ƙaunar Kiristi Yesu.
- Filibbiyawa 1:9kusan 64 M.
Addu’ata ita ce ƙaunarku tă yi ta cin gaba da ƙaruwa cikin sani da kuma zurfin ganewa,
- Filibbiyawa 1:10kusan 64 M.
don ku iya rarrabe abin da yake mafi kyau, ku kuma zama da tsarki, marasa aibi har yă zuwa ranar Kiristi,
- Filibbiyawa 1:11kusan 64 M.
cikakku da sakamakon aikin adalci da yake zuwa ta wurin Yesu Kiristi, zuwa ga ɗaukakar Allah da kuma yabonsa.
- Filibbiyawa 1:12kusan 64 M.
To, ina so ku sani ’yan’uwa, cewa abin da ya faru da ni ya sa cin gaban bishara.
- Filibbiyawa 1:13kusan 64 M.
Ta haka, ya zama sananne ga dukan masu gadin fada da kuma ga kowa cewa an daure ni da sarƙoƙi saboda Kiristi.
- Filibbiyawa 1:14kusan 64 M.
Saboda sarƙoƙina, yawancin ’yan’uwa cikin Ubangiji sun sami ƙarfafawa su yi maganar Allah gabagadi da kuma babu tsoro.
- Filibbiyawa 1:15kusan 64 M.
Gaskiya ce cewa waɗansu suna yin wa’azin Kiristi saboda kishi da neman faɗa, amma waɗansu da nufi mai kyau suke yi.
- Filibbiyawa 1:16kusan 64 M.
Na biye suna yin haka cikin ƙauna, da sanin cewa an sa ni a nan ne domin kāriyar bishara.
- Filibbiyawa 1:17kusan 64 M.
Na farin dai suna wa’azin Kiristi da sonkai ne, ba da zuciya ɗaya ba, a sonsu, su wahalar da ni a cikin sarƙoƙi.
- Filibbiyawa 1:18kusan 64 M.
Me kuma? Ta ko yaya dai, ko da gangan, ko da gaske, ana shelar Kiristi. Domin wannan kuwa ina farin ciki. I, zan kuwa ci gaba da farin ciki,
- Filibbiyawa 1:19kusan 64 M.
gama na san cewa ta wurin addu’o’inku da kuma taimako daga Ruhun Yesu Kiristi, abin da ya same ni zai zama sanadin kuɓutata.