circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Afisawa 5:27kusan 64 M.
Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani.
- Afisawa 5:28kusan 64 M.
Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne.
- Afisawa 5:29kusan 64 M.
Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,
- Afisawa 5:30kusan 64 M.
gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.
- Afisawa 5:31kusan 64 M.
“Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”
- Afisawa 5:32kusan 64 M.
Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya.
- Afisawa 5:33kusan 64 M.
Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.
- Afisawa 6:1kusan 64 M.
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan.
- Afisawa 6:2kusan 64 M.
Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, “Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,
- Afisawa 6:3kusan 64 M.
don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya.”
- Afisawa 6:4kusan 64 M.
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
- Afisawa 6:5kusan 64 M.
Ku bayi, ku yi biyayya ga iyayengijinku na duniya. Ku nuna musu halin bangirma, kuna kuma yin musu biyayya cikin dukan abu, da zuciya ɗaya kamar ga Kiristi kuke yi.
- Afisawa 6:6kusan 64 M.
Ku yi aiki sosai, ba don kawai ku gamshe su sa’ad da suke kallonku ba. Da yake ku bayin Kiristi ne, ku aikata nufin Allah da dukan zuciyarku.
- Afisawa 6:7kusan 64 M.
Ku yi aikinku da kyakkyawar niyya, sai ka ce ga Ubangiji kuke yi, ba mutane ba.
- Afisawa 6:8kusan 64 M.
Gama kun san cewa Ubangiji zai ba da lada ga kowa gwargwadon kowane aiki nagarin da ya yi, ko shi bawa ne, ko ’yantacce.
- Afisawa 6:9kusan 64 M.
Ku kuma masu bayi, dole ku bi da bayinku da kyau. Ku daina ba su tsoro. Ku tuna, ku da su, Maigida ɗaya kuke da shi a sama, kuma ba ya nuna bambanci.
- Afisawa 6:10kusan 64 M.
A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi.
- Afisawa 6:11kusan 64 M.
Ku yafa dukan kayan yaƙin da Allah yake bayarwa, don ku iya kāre kanku daga dabarun Shaiɗan.
- Afisawa 6:12kusan 64 M.
Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.
- Afisawa 6:13kusan 64 M.
Saboda haka sai ku yafa dukan kayan yaƙi na Allah, domin sa’ad da ranar mugun nan ta zo, ku iya yin tsayin daka, bayan kuma kuka gama kome, ku dāge.
- Afisawa 6:14kusan 64 M.
Saboda haka fa ku dāge, ku sa gaskiya tă zama ɗamararku, adalci yă zama sulkenku,
- Afisawa 6:15kusan 64 M.
shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.
- Afisawa 6:16kusan 64 M.
Ban da waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kibiyoyin wutar Mugun nan da ita.
- Afisawa 6:17kusan 64 M.
Ku kuma ɗauki hular kwano na ceto, da takobin Ruhu, wato, Maganar Allah.
- Afisawa 6:18kusan 64 M.
A koyaushe ku kasance kuna addu’a da roƙo ta wurin ikon Ruhu ba fasawa. A kan wannan manufa ku zauna a faɗake da matuƙar naci, kuna yin wa dukan mutanen Ubangiji addu’a.