Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Afisawa 4:9kusan 64 M.

    (Me ake nufin da “ya hau,” in ba cewa dā ya sauka can ƙarƙashin ƙasa ba?

  2. Afisawa 4:10kusan 64 M.

    Shi wannan da ya sauka ɗin, shi ne kuma ya hau zuwa can sama, kai, gaba da sammai, don mulkinsa yă cika duniya gaba ɗaya.)

  3. Afisawa 4:11kusan 64 M.

    Saboda haka Kiristi kansa ya ba wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu su zama annabawa, waɗansu su zama masu wa’azi, waɗansu kuma su zama fastoci, da kuma malamai.

  4. Afisawa 4:12kusan 64 M.

    Ya yi haka don yă shirya mutanensa saboda ayyukan hidima, don a gina jikin Kiristi.

  5. Afisawa 4:13kusan 64 M.

    Wannan zai ci gaba har sai mun zama ɗaya a cikin bangaskiya da kuma ta wurin fahimtarmu na Ɗan Allah. Sa’an nan za mu zama balagaggu, kamar yadda Kiristi yake, mu kuma zama gaba ɗaya cikakku kamar sa.

  6. Afisawa 4:14kusan 64 M.

    An yi wannan kuwa don kada mu koma zama kamar yara, muna ta canja zukatanmu game da abin da muka gaskata don kawai wani ya faɗa mana wani abu dabam, ko domin wani ya yi wayo ya ruɗe mu, ya sa ƙarya ta zama kamar gaskiya.

  7. Afisawa 4:15kusan 64 M.

    Ya kamata kullum ƙauna tă sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan

  8. Afisawa 4:16kusan 64 M.

    dukan jiki. Shi ne ya haɗe jiki duka, ya kuma sa dukan gaɓoɓin jiki suna aiki daidai, yayinda kowace gaɓa take aikinta cikin ƙauna.

  9. Afisawa 4:17kusan 64 M.

    To, ina dai faɗa muku, ina kuma nace faɗa muku a cikin Ubangiji, cewa kada ku ci gaba da yin rayuwa kamar yadda Al’ummai suke yi, masu banzan tunani.

  10. Afisawa 4:18kusan 64 M.

    Suna a cikin duhu a fahimtarsu, kuma a rabe suke daga ran Allah saboda jahilcin da yake cikinsu ta dalilin taurarewar zukatansu.

  11. Afisawa 4:19kusan 64 M.

    Ba sa damu da wani abu ko mai kyau ko marar kyau. Rayukansu sun cika da kowace irin ƙazanta da haɗama.

  12. Afisawa 4:20kusan 64 M.

    Amma ba abin da aka koya muku ke nan ba sa’ad da kuka zo ga sanin Kiristi.

  13. Afisawa 4:21kusan 64 M.

    Da yake kun ji duka game da shi, kuka kuma koyi gaskiyar da take cikin Yesu,

  14. Afisawa 4:22kusan 64 M.

    sai ku tuɓe tsohon mutumin nan naku da kuma rayuwarku ta dā, wadda take lalacewa saboda sha’awace-sha’awacen da suke ruɗe ku.

  15. Afisawa 4:23kusan 64 M.

    A maimakon haka, bari Ruhu yă sabunta tunaninku da kuma halayenku.

  16. Afisawa 4:24kusan 64 M.

    Ku sanya sabon halin nan da aka halitta bisa ga kamannin Allah, halin nan kuwa, yă bayyana cikin adalci, da zaman tsarki.

  17. Afisawa 4:25kusan 64 M.

    Saboda haka dole kowannenku yă bar yin ƙarya, yă kuma riƙa faɗa wa maƙwabcinsa gaskiya, gama dukanmu gaɓoɓi jiki ɗaya ne.

  18. Afisawa 4:26kusan 64 M.

    “Cikin fushinku kada ku yi zunubi.” Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,

  19. Afisawa 4:27kusan 64 M.

    kada kuma ku ba wa Iblis dama.

  20. Afisawa 4:28kusan 64 M.

    Duk wanda yake sata, sai yă daina sata, dole kuma yă yi aiki, yă yi wani abu mai amfani da hannuwansa, don yă sami abin da zai iya raba da masu bukata.

  21. Afisawa 4:29kusan 64 M.

    Kada wata ƙazamar magana ta fita daga bakunanku, sai dai abin da yake da amfani don gina waɗansu bisa ga bukatunsu. Ta haka maganarku za tă zama da amfani ga masu jinta.

  22. Afisawa 4:30kusan 64 M.

    Kada kuma ku ɓata wa Ruhu Mai Tsarki na Allah rai, wanda da shi aka hatimce ku da shi don ranar fansa.

  23. Afisawa 4:31kusan 64 M.

    Ku rabu da kowane irin ɗacin rai, haushi da hasala, faɗa da ɓata suna, ku rabu da kowace irin ƙeta.

  24. Afisawa 4:32kusan 64 M.

    Ku yi alheri, ku kuma ji tausayin juna, kuna gafarta wa juna, kamar yadda a cikin Kiristi, Allah ya gafarta muku.

  25. Afisawa 5:1kusan 64 M.

    Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya,