Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Afisawa 2:2kusan 64 M.

    Kun yi rayuwa kamar yadda sauran mutanen duniya suke yi, cike da zunubi, kuna biyayya ga sarki masu ikon sarari sama, wato, ruhun nan da yanzu yake aiki a cikin masu ƙin biyayya ga Allah.

  2. Afisawa 2:3kusan 64 M.

    Dukanmu a dā mun yi irin rayuwan nan a cikinsu, muna bin kwaɗayi da sha’awace-sha’awacen jikunanmu da tunaninmu. Kamar sauran mutane, mun cancanci fushin Allah.

  3. Afisawa 2:4kusan 64 M.

    Amma saboda yawan ƙaunar da yake mana, Allah, wanda yake mai yawan jinƙai,

  4. Afisawa 2:5kusan 64 M.

    ya ba mu rai sa’ad da ya tashe Kiristi daga matattu. Ta wurin alherin Allah ne aka cece ku.

  5. Afisawa 2:6kusan 64 M.

    Allah ya tashe mu tare da Kiristi, ya kuma ba mu wurin zama tare da shi a cikin mulkin samaniya.

  6. Afisawa 2:7kusan 64 M.

    Allah ya yi haka domin a tsararraki masu zuwa yă nuna yalwar alherinsa da ya wuce misali, an bayyana alheransa da ya yi mana ta wurin Kiristi Yesu.

  7. Afisawa 2:8kusan 64 M.

    Allah ya cece ku ta wurin alheri sa’ad da kuka ba da gaskiya. Wannan kuwa ba yinku ba ne, kyauta ce daga Allah.

  8. Afisawa 2:9kusan 64 M.

    Ba kuwa saboda aikin lada ba, don kada wani yă ɗaga kai.

  9. Afisawa 2:10kusan 64 M.

    Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.

  10. Afisawa 2:11kusan 64 M.

    Saboda haka, ku tuna dā ku Al’ummai ne bisa ga haihuwa, waɗanda kuma ake kira masu “kaciya” sukan kira ku “marasa kaciya” (ga shi kuwa, kaciyar nan ta jiki ce, wadda ake yi da hannu).

  11. Afisawa 2:12kusan 64 M.

    Ku kuma tuna a lokacin ba ku san Kiristi ba. A ware kuke daga mutanen Isra’ila, ba ku kuma da dangantaka da alkawaran da Allah ya yi da su. Kun yi zama a duniyan nan babu bege kuma babu Allah.

  12. Afisawa 2:13kusan 64 M.

    Amma yanzu a cikin Kiristi Yesu, ku da dā kuke can da nesa an kawo ku kusa ta wurin jinin Kiristi.

  13. Afisawa 2:14kusan 64 M.

    Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu.

  14. Afisawa 2:15kusan 64 M.

    Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.

  15. Afisawa 2:16kusan 64 M.

    A kan gicciye, Kiristi ya kawar da ƙiyayyar da take tsakaninmu da juna. Ya kuma kawo sulhu tsakaninmu da Allah.

  16. Afisawa 2:17kusan 64 M.

    Ya zo ya yi muku wa’azin salama; ku da kuke nesa da shi, ya kuma yi wa waɗanda suke kusa.

  17. Afisawa 2:18kusan 64 M.

    Gama ta wurinsa dukanmu za mu iya zuwa gun Uba ta wurin Ruhu guda.

  18. Afisawa 2:19kusan 64 M.

    Don haka, yanzu ku ba baƙi ba ne, ku kuma ba bare ba ne. Ku ’yan ƙasa ne tare da mutanen Allah, iyalin gidan Allah kuma.

  19. Afisawa 2:20kusan 64 M.

    Ku gini ne wanda manzanni da annabawa suke tushensa, Kiristi kuma shi ne dutse mafi muhimmanci na ginin.

  20. Afisawa 2:21kusan 64 M.

    Ta wurinsa ne dukan ginin yake a haɗe, shi ne kuma yake sa ginin yă yi girma, yă zama haikali mai tsarki domin Ubangiji.

  21. Afisawa 2:22kusan 64 M.

    Ku ma sashe ne na wannan ginin da Kiristi ya yi inda Allah yake zaune ta wurin Ruhunsa.

  22. Afisawa 3:1kusan 64 M.

    Saboda haka, ni Bulus, na zama ɗan kurkuku na Kiristi Yesu saboda ku Al’ummai.

  23. Afisawa 3:2kusan 64 M.

    Na tabbata kun ji labarin hidimar alheri na musamman da Allah ya ba ni dominku.

  24. Afisawa 3:3kusan 64 M.

    Wannan wasiƙa za tă faɗa muku kaɗan game da yadda Allah ya bayyana mini shirinsa na asiri.

  25. Afisawa 3:4kusan 64 M.

    A yayinda kuke karanta wannan, za ku gane abin da na sani game da wannan shirin Kiristi.