Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Afisawa 3:5kusan 64 M.

    Ba a sanar da wannan asiri wa wani a sauran zamanai ba, amma a yanzu an bayyana shi ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzanninsa da annabawansa.

  2. Afisawa 3:6kusan 64 M.

    Asirin nan kuwa shi ne cewa ta wurin bishara, Al’ummai sun zama waɗanda za su yi gādo tare da Isra’ila, sun zama gaɓoɓin jiki ɗaya, abokan tarayya kuma ga alkawaran nan a cikin Kiristi Yesu.

  3. Afisawa 3:7kusan 64 M.

    Na zama bawan wannan bishara ta wurin baiwar alherin Allah da aka yi mini ta wurin ikonsa da yake aiki a cikina.

  4. Afisawa 3:8kusan 64 M.

    Ko da yake ni ba kome ba ne a cikin dukan mutanen Ubangiji, aka ba ni wannan baiwa mai daraja don in faɗa wa Al’ummai cewa saboda Kiristi akwai albarkun da suka wuce gaban misali.

  5. Afisawa 3:9kusan 64 M.

    An zaɓe ni in bayyana wa dukan mutane shirin asirin nan wanda Allah, mahaliccin kome, ya ɓoye shekara da shekaru.

  6. Afisawa 3:10kusan 64 M.

    Nufinsa shi ne, yanzu, ta wurin ikkilisiya, a sanar da hikima iri dabam-dabam na Allah ga masu mulki, da masu iko a samaniya.

  7. Afisawa 3:11kusan 64 M.

    Wannan shi ne madawwamin shirinsa, kuma an aikata shi ta wurin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  8. Afisawa 3:12kusan 64 M.

    A cikinsa, kuma ta wurin bangaskiya a cikinsa ne muke da ƙarfin halin zuwa kusa da Allah gabagadi.

  9. Afisawa 3:13kusan 64 M.

    Don haka, ina roƙonku kada ku fid da zuciya saboda abin da ake yi mini a nan. Ai, saboda ku ne nake shan wahalolin nan, wannan kuwa ɗaukakarku ce.

  10. Afisawa 3:14kusan 64 M.

    Saboda wannan ne nake a durƙushe a gaban Uba,

  11. Afisawa 3:15kusan 64 M.

    wanda ya ba wa kowane iyali a sama da ƙasa suna.

  12. Afisawa 3:16kusan 64 M.

    Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.

  13. Afisawa 3:17kusan 64 M.

    Ina addu’a domin Kiristi yă zauna a cikin zukatanku ta wurin bangaskiya. Ina kuma addu’a saboda ku da kuka kahu sosai cikin ƙauna,

  14. Afisawa 3:18kusan 64 M.

    don ku sami iko, tare da dukan tsarkaka, ku fahimci fāɗi, tsawo, da kuma zurfin ƙaunar Kiristi take.

  15. Afisawa 3:19kusan 64 M.

    Ku kuma san wannan ƙauna wadda ta fi gaban sani, domin a cika ku da dukan cikar Allah.

  16. Afisawa 3:20kusan 64 M.

    Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi shi wanda yake da ikon yin aiki a cikinmu, yana kuma aikata abubuwa fiye da dukan abin da muke roƙo, ko muke tunani.

  17. Afisawa 3:21kusan 64 M.

    Bari ɗaukaka ta tabbata a gare shi a cikin ikkilisiya da kuma a cikin Kiristi Yesu, har yă zuwa dukan zamanai, har abada abadin! Amin.

  18. Afisawa 4:1kusan 64 M.

    A matsayina na ɗan kurkuku saboda Ubangiji, ina roƙonku ku yi rayuwar da ta dace da kiran da aka yi muku.

  19. Afisawa 4:2kusan 64 M.

    Kullum ku kasance masu sauƙinkai da kuma hankali; ku zama masu haƙuri, kuna jimrewa da juna cikin ƙauna.

  20. Afisawa 4:3kusan 64 M.

    Ku yi ƙoƙari sosai ku kiyaye zaman ɗayan nan da Ruhu ya ba ku, ku yi haka ta wurin zaman lafiya da juna.

  21. Afisawa 4:4kusan 64 M.

    Dukanku jiki ɗaya ne, kuna kuma da Ruhu guda. An ba ku bege guda sa’ad da aka kira ku.

  22. Afisawa 4:5kusan 64 M.

    Ubangiji ɗaya, bangaskiya ɗaya, baftisma kuma ɗaya,

  23. Afisawa 4:6kusan 64 M.

    Allah ɗaya Uban duka, wanda yake a bisa duka, ta wurin duka, a cikin duka kuma.

  24. Afisawa 4:7kusan 64 M.

    Amma ga kowannenmu an ba da alheri bisa ga yadda Kiristi ya rarraba.

  25. Afisawa 4:8kusan 64 M.

    Shi ya sa aka ce, “Sa’ad da ya hau sama, ya bi da kamammu kamar tawagarsa ya kuma ba da baye-baye ga mutane.”