circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Afisawa 5:2kusan 64 M.
ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
- Afisawa 5:3kusan 64 M.
Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.
- Afisawa 5:4kusan 64 M.
Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
- Afisawa 5:5kusan 64 M.
Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
- Afisawa 5:6kusan 64 M.
Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
- Afisawa 5:7kusan 64 M.
Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
- Afisawa 5:8kusan 64 M.
Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske
- Afisawa 5:9kusan 64 M.
(domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya)
- Afisawa 5:10kusan 64 M.
ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
- Afisawa 5:11kusan 64 M.
Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.
- Afisawa 5:12kusan 64 M.
Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
- Afisawa 5:13kusan 64 M.
Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.
- Afisawa 5:14kusan 64 M.
Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
- Afisawa 5:15kusan 64 M.
Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.
- Afisawa 5:16kusan 64 M.
Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
- Afisawa 5:17kusan 64 M.
Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
- Afisawa 5:18kusan 64 M.
Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
- Afisawa 5:19kusan 64 M.
Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.
- Afisawa 5:20kusan 64 M.
Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
- Afisawa 5:21kusan 64 M.
Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
- Afisawa 5:22kusan 64 M.
Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.
- Afisawa 5:23kusan 64 M.
Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.
- Afisawa 5:24kusan 64 M.
To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.
- Afisawa 5:25kusan 64 M.
Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.
- Afisawa 5:26kusan 64 M.
Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.