circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Galatiyawa 5:19kusan 58 M.
Ayyukan mutuntaka kuwa a fili suke. Wato, fasikanci, ƙazanta da kuma lalata;
- Galatiyawa 5:20kusan 58 M.
bautar gumaka da sihiri; ƙiyayya, faɗa, kishi, fushi mai zafi, sonkai, tsattsaguwa, hamayya,
- Galatiyawa 5:21kusan 58 M.
da ƙyashi; buguwa, shashanci, da ire-irensu. Na gargaɗe ku, yadda na yi a dā, cewa masu irin wannan rayuwa ba za su gāji mulkin Allah ba.
- Galatiyawa 5:22kusan 58 M.
Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci,
- Galatiyawa 5:23kusan 58 M.
sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
- Galatiyawa 5:24kusan 58 M.
Waɗanda suke na Kiristi Yesu, sun gicciye mutuntaka tare da abubuwan da mutum yake marmari da kuma sha’awace-sha’awacensa.
- Galatiyawa 5:25kusan 58 M.
Da yake muna rayuwa ta Ruhu ne, bari mu ci gaba da al’amuranmu ta wurin Ruhu.
- Galatiyawa 5:26kusan 58 M.
Kada mu zama masu girman kai, muna tsokana muna kuma jin kishin juna.
- Galatiyawa 6:1kusan 58 M.
’Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.
- Galatiyawa 6:2kusan 58 M.
Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.
- Galatiyawa 6:3kusan 58 M.
In wani yana tsammani shi wani abu ne alhali kuwa shi ba kome ba, ruɗin kansa yake yi.
- Galatiyawa 6:4kusan 58 M.
Kowa yă auna ayyukansa. A sa’an nan ne zai iya yin taƙama da kansa, ba tare da kwatanta kansa da wani ba,
- Galatiyawa 6:5kusan 58 M.
gama kowa zai ɗauki kayansa.
- Galatiyawa 6:6kusan 58 M.
Duk haka, wanda aka koya wa maganar Kiristi, bari yă raba abubuwan nan na alheri tare da wanda ya koyar da shi.
- Galatiyawa 6:7kusan 58 M.
Kada a ruɗe ku. Ba a yi wa Allah ba’a. Mutum yakan girbe abin da ya shuka ne.
- Galatiyawa 6:8kusan 58 M.
Wanda ya yi shuki don yă gamshi mutuntakarsa, daga wannan mutuntaka zai girbi hallaka. Wanda ya yi shuki domin yă gamshi Ruhu, daga Ruhu zai girbi rai madawwami.
- Galatiyawa 6:9kusan 58 M.
Kada mu gaji da yin nagarta, gama a daidai lokaci za mu girbe amfani, in ba mu fid da zuciya ba.
- Galatiyawa 6:10kusan 58 M.
Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.
- Galatiyawa 6:11kusan 58 M.
Ku dubi irin manya-manyan harufan da na yi amfani da su yayinda nake rubuta muku da hannuna!
- Galatiyawa 6:12kusan 58 M.
Waɗanda suke son nuna bajinta a fili suna ƙoƙari su tilasta muku ku yi kaciya ne. Dalilin kaɗai da suke yin haka shi ne don gudu kada a tsananta musu saboda gicciyen Kiristi ne.
- Galatiyawa 6:13kusan 58 M.
Kai, su masu kaciya ma ba su kiyaye Doka ba, duk da haka suna so a yi muku kaciya don su yi taƙama kan an yi muku kaciya.
- Galatiyawa 6:14kusan 58 M.
Kada in taɓa yin taƙama ga kome sai dai a cikin gicciyen Ubangijinmu Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa aka gicciye duniya a gare ni, aka kuma gicciye ni ga duniya.
- Galatiyawa 6:15kusan 58 M.
Kaciya ko rashin kaciya ba wani abu ba ne; abin da yake da amfani shi ne sabuwar halitta.
- Galatiyawa 6:16kusan 58 M.
Salama da jinƙai su tabbata ga dukan waɗanda suke bin wannan ƙa’ida, har ma ga Isra’ila na Allah.
- Galatiyawa 6:17kusan 58 M.
A ƙarshe, kada kowa yă ƙara damuna, gama ina ɗauke da raunuka masu nuna ni bawan Ubangiji Yesu ne.