circa AD 48–96
Letters to the Churches
Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.
Ayoyi daga wannan lokacin
- Galatiyawa 3:29kusan 58 M.
In kuwa ku na Kiristi ne, to, ku zuriyar Ibrahim ne, magāda kuma bisa ga alkawarin nan.
- Galatiyawa 4:1kusan 58 M.
Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.
- Galatiyawa 4:2kusan 58 M.
Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.
- Galatiyawa 4:3kusan 58 M.
Haka yake, sa’ad da muke ’yan yara, mun kasance cikin bauta a ƙarƙashin ƙa’idodin duniya.
- Galatiyawa 4:4kusan 58 M.
Amma da lokacin da aka tsara ya yi sosai, sai Allah ya aiki Ɗansa, haifaffe daga mace, haifaffe a ƙarƙashin Doka,
- Galatiyawa 4:5kusan 58 M.
domin yă fanshi waɗanda suke a ƙarƙashin doka, saboda mu sami cikakken matsayin zaman ’ya’ya.
- Galatiyawa 4:6kusan 58 M.
Da yake ku ’ya’ya ne, sai Allah ya aiko da Ruhun Ɗansa a cikin zukatanmu, Ruhun da yake kira, “Abba, Uba.”
- Galatiyawa 4:7kusan 58 M.
Saboda haka kai ba bawa ba ne kuma, kai ɗa ne; da yake kuwa kai ɗa ne, Allah ya mai da kai magāji.
- Galatiyawa 4:8kusan 58 M.
Dā da ba ku san Allah ba, ku bayi ne ga waɗanda a ainihi ba alloli ba ne.
- Galatiyawa 4:9kusan 58 M.
Amma yanzu da kuka san Allah, ko kuma a ce Allah ya san ku, yaya kuke sāke komawa ga ƙa’idodin duniya marasa ƙarfi, abin tausayi kuma? Kuna so ku sāke komawa ga bautarsu ne?
- Galatiyawa 4:10kusan 58 M.
Kuna kiyaye ranaku da watanni da lokuta da shekaru na musamman!
- Galatiyawa 4:11kusan 58 M.
Kai, kun ba ni tsoro, don ya zama kamar duk wahalar da na yi a kanku banza ne!
- Galatiyawa 4:12kusan 58 M.
Ina roƙonku ’yan’uwa, ku zama kamar ni, gama na zama kamar ku. Ba ku yi mini wani laifi ba.
- Galatiyawa 4:13kusan 58 M.
Kun san rashin lafiyar da na yi, shi ne ya yi mini hanyar da na kawo muku bishara da farko.
- Galatiyawa 4:14kusan 58 M.
Ko da yake ciwona gwaji ne gare ku, ba ku yi mini reni ko ƙyama ba. A maimakon haka, kuka karɓe ni sai ka ce mala’ikan Allah, kuma sai ka ce Kiristi Yesu kansa.
- Galatiyawa 4:15kusan 58 M.
Me ya faru da dukan farin cikinku? Na tabbata, a lokacin, da mai yiwuwa ne da kun ciccire idanunku kun ba ni.
- Galatiyawa 4:16kusan 58 M.
Yanzu na zama abokin gābanku don na faɗa muku gaskiya ke nan?
- Galatiyawa 4:17kusan 58 M.
Waɗancan mutane suna neman su rinjaye ku da ƙwazo, amma ba da kyakkyawar aniya ba. Abin da suke so shi ne su raba ku da mu, saboda ƙwazonku yă koma gare su.
- Galatiyawa 4:18kusan 58 M.
Yana da kyau ku kasance da irin wannan niyya idan da nufi mai kyau ne, ku kuma kasance a haka koyaushe ba sai ina tare da ku ba.
- Galatiyawa 4:19kusan 58 M.
Ya ku ’ya’yana ƙaunatattu, ina sāke shan wahalar naƙudarku, har sai Kiristi ya kahu a cikinku.
- Galatiyawa 4:20kusan 58 M.
Da ma a ce ina tare da ku yanzu in canja muryata mana! Gama na damu ƙwarai saboda ku!
- Galatiyawa 4:21kusan 58 M.
Ku gaya mini, ku da kuke so ku zauna a ƙarƙashin Doka, ba ku san abin da Doka ta ce ba ne?
- Galatiyawa 4:22kusan 58 M.
Gama a rubuce yake cewa Ibrahim yana da ’ya’ya biyu maza, ɗaya ta wurin mace ’yar aikin gidansa, ɗaya kuma ta wurin ainihin matarsa.
- Galatiyawa 4:23kusan 58 M.
Ɗansa na wajen mace ’yar aikin gidansa ya zo bisa ga ƙa’idar jiki ne; amma ɗansa na wajen ainihin matarsa ya zo a sakamakon alkawarin ne.
- Galatiyawa 4:24kusan 58 M.
Za a iya ɗaukan waɗannan al’amura a matsayin misali, domin matan nan suna misalta alkawura biyu ne. Alkawari ɗaya daga Dutsen Sinai ne yana kuma haihuwar ’ya’yan da za su zama bayi. Hagar ke nan.