Tsallake zuwa abun ciki

circa AD 48–96

Letters to the Churches

Paul and other apostles write to strengthen, correct, and encourage the scattered churches across the Roman world.

2,767 ayoyi · 21 littattafai da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

Tace bisa littafi
  1. Galatiyawa 4:25kusan 58 M.

    Hagar tana a matsayin Dutsen Sinai a Arabiya tana kuma kwatancin birnin Urushalima na yanzu, gama ita baiwa ce tare da ’ya’yanta.

  2. Galatiyawa 4:26kusan 58 M.

    Amma Urushalimar da take sama ’yantacciya ce, ita ce kuma mahaifiyarmu.

  3. Galatiyawa 4:27kusan 58 M.

    Gama a rubuce yake cewa, “Ki yi farin ciki, ya ke bakararriya, wadda ba ta haihuwa ki ɓarke da murna, ki kuma tā da murya, ke da ba kya naƙuda; domin da yawa ne ’ya’yan macen da aka yashe, fiye da na mai miji.”

  4. Galatiyawa 4:28kusan 58 M.

    To, ku ’yan’uwa, ku ’ya’yan alkawari ne kamar Ishaku.

  5. Galatiyawa 4:29kusan 58 M.

    A wancan lokaci, wannan ɗa wanda aka haifa ta wurin ƙa’idar jiki ya tsananta wa wanda aka haifa ta ikon Ruhu. Haka ma yake har yanzu.

  6. Galatiyawa 4:30kusan 58 M.

    Amma me Nassi ya ce? Nassi ya ce, “Kori macen nan ’yar aikin gida da ɗanta don ɗan mace ’yar aikin gida ba zai taɓa raba gādo tare da ɗa na ainihin matarka ba.”

  7. Galatiyawa 4:31kusan 58 M.

    Saboda haka, ’yan’uwa, mu ba ’ya’yan mace ’yar aikin gida ba ne, amma na ainihin matan gidan ne.

  8. Galatiyawa 5:1kusan 58 M.

    Saboda ’yanci ne Kiristi ya ’yantar da mu. Sai ku tsaya daram, kada ku yarda ku sāke komawa ƙarƙashin nauyin bauta.

  9. Galatiyawa 5:2kusan 58 M.

    Ku lura da kalmomina! Ni Bulus ina gaya muku cewa in kuka yarda aka yi muku kaciya, wannan ya nuna Kiristi ba shi da amfani a gare ku ba ko kaɗan.

  10. Galatiyawa 5:3kusan 58 M.

    Haka kuma ina ƙara sanar wa kowane mutumin da ya yarda aka yi masa kaciya cewa dole yă kiyaye dukan Doka.

  11. Galatiyawa 5:4kusan 58 M.

    Ku da kuke ƙoƙarin kuɓuta ta wurin Doka an raba ku da Kiristi ke nan; kuka kuma fāɗi daga alheri.

  12. Galatiyawa 5:5kusan 58 M.

    Amma ta wurin bangaskiya muna marmarin jira adalcin da muke bege ta wurin Ruhu.

  13. Galatiyawa 5:6kusan 58 M.

    Gama a cikin Kiristi Yesu, kaciya ko rashin kaciya ba su da wani amfani. Abin da kawai yake da amfani shi ne, bangaskiyar da take bayyana kanta ta wurin ƙauna.

  14. Galatiyawa 5:7kusan 58 M.

    Kun yi tsere mai kyau a dā. Wa ya shige gabanku ya hana ku bin gaskiya?

  15. Galatiyawa 5:8kusan 58 M.

    Wannan rarrashin da ake muku ba daga wanda ya kira ku ba ne.

  16. Galatiyawa 5:9kusan 58 M.

    “Ɗan yisti kaɗan ne yake gama dukan curin burodi.”

  17. Galatiyawa 5:10kusan 58 M.

    Ina da tabbaci cikin Ubangiji cewa ba za ku bi wani ra’ayi dabam ba. Wannan da yake rikita ku za a hukunta shi, ko shi wane ne.

  18. Galatiyawa 5:11kusan 58 M.

    ’Yan’uwa, da a ce har yanzu ina wa’azin kaciya ne, to, me ya sa ake tsananta mini har yanzu? In haka ne, ashe, an kawar da abin da yake sa tuntuɓe game da gicciye ke nan.

  19. Galatiyawa 5:12kusan 58 M.

    Da ma a ce masu tā da hankalinku ɗin nan su yanke gabansu gaba ɗaya mana!

  20. Galatiyawa 5:13kusan 58 M.

    Ku ’yan’uwana, an kira ku ga zama ’yantattu. Amma kada ku yi amfani da ’yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.

  21. Galatiyawa 5:14kusan 58 M.

    Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

  22. Galatiyawa 5:15kusan 58 M.

    In kun ci gaba da cizo, kuna kuma cin naman juna, ku yi hankali in ba haka ba za ku hallaka juna.

  23. Galatiyawa 5:16kusan 58 M.

    Saboda haka ina ce muku, ku yi rayuwa ta wurin Ruhu, ba za ku kuwa gamsar da sha’awace-sha’awacen mutuntaka ba.

  24. Galatiyawa 5:17kusan 58 M.

    Gama mutuntaka yana son abin da Ruhu yake ƙi, Ruhu kuma yana son abin da mutuntaka yake ƙi. Waɗannan biyu kuwa gāba suke da juna, har ku kāsa yin abin da kuke so.

  25. Galatiyawa 5:18kusan 58 M.

    Amma in Ruhu ne yake bishe ku, ba ku a ƙarƙashin Doka ke nan.